HKI Ta Kashe Falasdinawa 8 A Gaza A Yau Asabar

Akalla falasdinawa 8 ne suka yi shahada sanadiyyar hare haren da sojojin HKI suka kai kan falasdinawa a zirin Gaza, a yayinda wasu da dama

Akalla falasdinawa 8 ne suka yi shahada sanadiyyar hare haren da sojojin HKI suka kai kan falasdinawa a zirin Gaza, a yayinda wasu da dama suka ji rauni, wanda kuma ya kawo yawan Falasdinawa wanda aka kashe a gaza tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa kimani 73,350.

Kamfanin dillancin labaran shehab na kasar Iran ya nakalto majiyar asbitocin Gaza na cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata, falasdinawa akalla 8 ne suka yi shahada a yayinda wasu 76 suka ji rauni a duk fadin zirin gaza a hare haren da yahudawan HKI suka kai a yankuna daban daban.

Labarin ya kara da cewa tun bayan fara yakin tufanul Aksa falasdinawa akalla 174,162 ne suka ji rauni. Sanna idan an yi lissafain wadanda suka yi shahada  tun bayan tsagaita wuta a ranar 11 ga watan Octoban shekara ta 2025 kuma, adadinsu ya kai 1,222, sannan wasu 4,053 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted