Qalibaf: Amurka Ta Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Saboda Kai Hare Hare A Kan Tsibirin Qeshm

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibof ya sha alwashin maida martani mai tsanani kan sojojin Amurka da kadarorinta da suke yankin yammacin Asia

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibof ya sha alwashin maida martani mai tsanani kan sojojin Amurka da kadarorinta da suke yankin yammacin Asia saboda hare haren da suka kai kan tsibirin Qeshm na kasar Iran da ke cikin tekun farisa.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto qalibof yana fadar haka a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya kuma kara da cewa, Amurka ta aikata wani aikin ta’addanci babba kan fararen hula a tsibirin Qeshm na kasar Iran wanda ci gaba ne da irin ayyukan ta’addancinci da ta aikata a garin Minab na lardun Humurgan a farkon wannan shekara.

Yace Amurka tana aikata wadan nan ayyukan ta’addanci ne a duk lokacinda sojojin Iran sun yi masu duka mai tsanani a yakin da suke fafatwa da ita. Ya kuma kammala da cewa a wannan karon ma zata gamu da maida martani mai tsanani.

Kafin haka dai, jiragen yakin Amurka sun kai hare hare kan tsibirin Qsem, ba Bushahr, da lardin Fars da kuma lardin Khuzestan duk nab akin tekun farisa. Mafi muni da cikin hare haren shi ne wanda ya fada kan wani gida a tsibirin Qeshm ya kuma kashe mutane 3 a gida guda, uba da Uwa da kuma daya da cikin yayansu. Sauran yayan yan agaji sun fiddasu karkashin burbushin gine gina da rayukansu. A halin yanzun suna jinya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted