Wani Babban Sojan Amurka Ya Bayyana Cewa Kasar Bata Da Makaman Kare HKI

Kwamandan sojojin Amurka a turai wato ‘ U.S. European Command’ ya fadawa ma’aikayar yakin Amurka PENTAGON kan cewa karancin garkuwan makamai a sashen sojojin ruwa

Kwamandan sojojin Amurka a turai wato ‘ U.S. European Command’ ya fadawa ma’aikayar yakin Amurka PENTAGON kan cewa karancin garkuwan makamai a sashen sojojin ruwa na kasar ya sa shi dole ya zabi kare sojojin Amurka daga makaman masu linzami samfurin balistic na kasar Iran maimakon kare sojojin HKI.

Jaridar washigton Post ta nakalto Janar Greenwich babban kwamandan sojojin Amurka a kasashen turai yana cewa, ya gargadi ma’aikatar yakin Amurka Pentagon kan cewa, ya gargadi ma’aikatar kan cewa, karancin garkuwan makamai masu linzami zasu sashi yak are Amurka kadai ba tare da kare HKI daga makaman Iran.

Kwamandan yace ya aikawa Pentagon a rubuce kan cewa, ba tare da jirgin yakin na ruwa ba, bai da zabi in banda kare sojojin Amurka kadai a yakin da take fafatawa da Iran.

Janar Greenwich ya shaida jaridar kan cewa a halin yanzu karancin makamai ya kaiga dole sai sun zabi wanda zasu kare, a tsakanin Amurka da HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted