Mutane 22 ne suka mutu, yawancinsu dalibai, bayan da wani gini ya rufta a Tarayyar Najeriya
Akalla mutane 22 ne suka mutu, yawancinsu dalibai, yayin da wasu da dama suka jikkata a jiya Juma’a, bayan da wani gini mai hawa biyu ya rufta a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.
Kafafen yada labarai sun rawaito daga kakakin ‘yan sandan jihar cewa: Mutane 154 ne suka makale a karkashin baraguzan ginin, kuma an ceto kowa da kowa banda wadanda suka mutu, sannan an kai su zuwa asibitocin da suke kusa, inda kakakin ‘yan sandan ya ce; Akasarin wadanda abin ya ritsa da su dalibai ne da kuma ma’aikatan makarantar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto daga kungiyar agaji ta Red Cross cewa: Dalibai 21 ne suka mutu a hatsarin, yayin da wasu 69 na daban suka jikkata, wadanda aka kai su asibitoci daban-daban domin jinya.
Ba a dai bayyana musabbabin rugujewar ginin ba, amma mazauna yankin sun ce: Hatsarin ya faru ne bayan kwanaki 3 da yin ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin.