Wani jami’in kasar Ukiraniya ya bayyana cewa, a kalla mutane 8 ne su ka jikkata sanadiyyar munanan hare-haren da Rasha ta kai wa birnin Kiev ta hanyar amfani da makamai masu linzami.
Shugaban sha’anin tafiyar da Mulki na soja a birnin Kiev Taimur Tikatishinko ya wallafa sanarwa a shafinsa na “Telegram’ cewa; A tsakanin wadanda su ka jikkata din da akwai karamin yaro dan shekaru 3, kuma tuni an dauki mutane 4 zuwa asibiti, daya daga cikinsu yana cikin mummunan hali.
Shi kuwa magajin birnin na Kiev Fitali Kikitshiko cewa ya yi, mutanen da su ka jikkata suna zaune ne a cikin gidaje mabanbanta a unguwa daya.
Har ila yau ya kara da cea; Harin ya haddasa fashewa mai karfi wacce ta sa tagogin gidaje su ka fashe, har zuwa gine-gine masu hawa 11.
A wani labarin daga jami’an kasar ta Ukiraniya, Rasha ta kai wasu hare-haren da jirage marasa matuki a garin Kirofifitsky wanda ya haddasa fashewa mai yawa.
A cikin makwannin bayan nan dai Rasha ta tsananta kai hare-hare a fadin kasar Ukiraniya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.
Tun a 2022 ne dai Rasha ta fara kai wa Ukiraniya hare-hare bisa dalilin cewa tana son shiga cikin kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.
Kasar ta Ukiraniya dai tana samun taimakon makamai da bayanai na sirri daga kungiyar ta Nato.