Rahoto: Yara Falasdinawa 350 ne Isra’ila ke tsare da su a gidajen kurkuku

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni.

Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita.

Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon nan a gidan yarin Isra’ila.

A cewar wadannan kungiyoyi, tsare yara bias irin wannan tsari na Isra’ila yana karuwa, kuma manufarsu ita ce kawar da yaran daga cikin iyalansu da lalata kuruciyarsu. Kuma wannan shi ne a lokacin da aka fi kai hare-hare mafi muni a tarihi kan yaran Palastinawa, yayin da ake ci gaba da kisan kiyashin, dubban yara ne suka yi shahada, wasu dubbai kuma suka jikkata ko kuma sun rasa iyalansu.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun kuma sanar da cewa, tun bayan da aka fara kisan kiyashin, an samu sauye-sauye a halin da ake ciki na fursunoni yara.

Game da yara a Gaza, saboda ci gaba da tilsta manufar korar jama’a daga yankunansu da Isra’ila ke aiwatarwa, yara da dama sun rabu da iyalansu.

Duk da tsauraran matakan hana kai ziyara, kungiyoyin lauyoyi sun yi nasarar ganawa da wasu daga cikin yaran da ake tsare da su a gidajen yarin Ofer, Megiddo, da Damon, kuma an tattara shedu da dama da suka nuna irin yadda ake azabtar da su da kuma tauye hakki akan wadannan yaran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments