Kasashen Faransa Masar Da Jordan Sun Yi Taro Akan Gaza

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin alkahira a jiya Lahadi, inda ya sami kyakkyawar tarba daga Abdulfattah al-Sisi. Ziyarar ta shugaban kasar Faransa a Masar tana a karkashin tattaunawar da aka bude ne a yau Litinin tare da kasar Jordan da kuma ita kanta mai masaukin baki akan halin da Gaza take ciki. […]

 HKI Ta Kai Munanan Hare-hare Akan Yankin Khan-Yunus

A rana ta 21 da Isra’ila ta sake komawa yaki da al’ummar Falasdinu a Gaza, jiragen yakinta sun kai hare-hare munanan a yankin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da kuma jikkata wani adadin Falasidinawa  mai yawa. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai kungiyar  Hamas ta mayar da martani ta […]

Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun kira jakadunsu daga Aljeriya

Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi […]

Iran : kasashen turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyan bayan Isra’ila

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar […]

Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Yemen

Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Yemen, inda ta kai sabbin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar a baya bayan nan. Kafar yada labaran kasar Yemen ta bayyana cewa, Amurka ta kai akalla hare-haren jiragen yaki guda uku a gundumar Bani Matar da ke lardin Sanaa. Akalla fararen hula hudu ne […]

Gaza : adadin ‘yan jaridar da aka kashe ya haura 210

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari […]

Araqchi: Babu Wata Tattaunawa Da Aka Gudanar Tsakanin Amurka Da Iran

Iran ta sake nanata matsayinta na kin shiga shawarwari kai tsaye da Amurka kan shirinta na nukiliya, maimakon haka ta bukaci a ci gaba da shawarwarin ta hanyar masu shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wata tattaunawa da aka da Washington, kuma ba za a yi […]

Hassan Fadlallah: Amurka ke da alhakin ayyukan wuce gona da iri na Isr’aila a Lebanon

Wani mamba na kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya soki hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila take kai wa a kudancin kasar Lebanon da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai jaddada cewa Amurka ce ke da alhakin kai hare-haren wuce gona da iri na sahyoniyawan. A cewar Al-Mayadeen, mazauna kudancin […]

An sake kona Kur’ani mai tsarki a kasar Netherlands

Edwin Wagensfeld, mai tsattsauran ra’ayi mai tsattsauran ra’ayi kuma mai magana da yawun kungiyar Pegida ta kasar Holland, ya kona kur’ani a gaban zauren majalisa a birnin Amsterdam, a wani mataki na nuna kyama ga Musulunci, kuma wannan matakin ya haifar da fushin ‘yan siyasa da ‘yan kasar ta Holland. A cewar gidan talabijin na […]

Rahoto: Yara Falasdinawa 350 ne Isra’ila ke tsare da su a gidajen kurkuku

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da […]

ACF Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Kawo Karshe Tashe-Tashen Hankula Filato

Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da […]