Qatar Ta Ce Bata Goyon Bayan Yakin Don Warware Shirin Nukliyar Kasar Iran

Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani, ya kara nanata matsayin kasar na kin duk wani yaki kan shirin Nukliyar kasar Iran, ya

Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani, ya kara nanata matsayin kasar na kin duk wani yaki kan shirin Nukliyar kasar Iran, ya kuma yi kira ga Amurka da Iran su warware wannan matsalar ta ruwan sanyi. Ko hanyar diblomasiyya.

Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa shirinta na makamashin na zaman lafiya ne. Sannan don haka ne ta amince ta kulla yarjeniyar shirin nukliya ta zaman lafiya  da manya manyan kasashen duniya, a shekara ta 2015 daga ciki har da kasar Amurka. Amma shugaban kasar Amurka na lokacin Donql Trump ta fidda kasar daga yarjeniyar sannan ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni don tursasa mata ta sake zama don sabuwar tattaunawa da ita.

Mohammed bin Abdulrahman Al Thani yace “akwai bukatar kasashen Iran da Amurka su fahinci juna a cikin wannan batun” sannan ya sake nanata cewa Qatar bata goyon bayan yaki. Sannan daga karshe yace matsalar nukliyar kasar Iran ta zama abinda damuwa ga dukkan kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments