Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata dawo daga hakkinta na iko da mashigar ruwa ta Hurmuz ba, saboda na farko hakkinta ne wani bangare ne na kasar Iran.
Tashar talabijan ta Presstv a nnan ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a hira da yayi da tashar talabijan ta ‘Khabar’ a yau Talaba ya kuma kara da cewa mashigar hakkin mutanen kasar Iran ne wanda All..ya mayar masu bayan hare-haren ta’addanci wadanda Amurka da HKI suka dorawa kasar a karshen watan Fabrayrun da ya gabata.
Ya ce a halin yanzu kasar Iran tana kara tsananta riko da mashigar don ta gano cewa babban makami ni kan makiyanta, musamman bayan tsokana da kuma zaluncin da suka yi wa mutanen kasar shekaru kimani 50 da suka gabata.
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana ce wa, a halin yanzun mun bude mashigar na wucin gadi ne, don haka bama son Amurka ta samar da wani rikici da kuma rashin fahinta, inda take nuna cewa Iran ta toshe mashigar da makamai al-hali a bude take a baya.
Yace aya ta 5 na yarjeniyar Fahintar juna tsakaninta da Amurka ya tabbatar da cewa, mashigar ruwa ta Hurmuz mallakin Iran da Omman ne, sannan sune zasu ci gaba da gudanar da al-amuran mashigar kamar yanda yake a fahintar juna na 7 ga watan Afrilu.