06-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci a cikin tarihi’ shiri wanda yake kawo maku al-adu da ci gaban da addinin musulunci ya samu tun bayan bayyanarsa ya zuwa yanzu, wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasace tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…Masu, sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun karasa magana kan rayuwar larabawa kafin bayyanar addinin musulunci, sannan mu bayyana cewa All..T yayi masu ni’ima ya kuma yiwa sauran mutane a duniya ni’ima inda ya aiko Manzon a cikinsu ya kuma aiko da shiriya ta sabuwar rayuwa a cikinsu.
Ya aiko da Manzon All..(s) a birnin Makka, wanda ya kirasu zuwa gaskiya, zuwa sabuwar rayuwa ta mutunci da alkhairi duniya da Lahira.
Sannan ya ci gaba da kiransu zuwa wannan addinin da sabon rayuwa na tsawon shekaru 13 a makka, amma sun ki amsa kirinsa sai yan tsiraru, su dimma basu barsu ba, sun yi ta azabtar da su, sun kashe wasu, har sai da ya ga ba makawa sai ya bar Makka ya koma wani wuri don kafa daular musulunci ta farko.
Mun bayyana yadda, da farko ya tura wasu daga cikin sahabbansa zuwa kasar Habasha nesa da Makka, don su rayuwa nesa da Mushirin kan Makka, amma wannan bai wadatar ba. Sai da y afara neman wani wurin da shi da sauran sahabban nasa zasu koma don rayuwa cikin sauki da kuma dabbaka sabon addinin da ya zo da shi a cikin nutsuwa da kuma zaman lafiya.
Da farko ya je wani gari kusa da Makka, wato Ta’ifa inda suka mayar masa da mummuna, suka jefeshi har suka zubar da jininsa. Sannan daga baya ya hadu da mutanen Madina wato Hazraj da Aus, wasunsu ska fara musulunta, a lokacin aikin hajja, sannan a wata shekarar yawansu ya karu. A lokacinda aka yi bai’ar Aqaba na biyu ya samu mafi yawan mutanen madina ko Yathriba a lokacin sun musulunta.
Sannan umrnin ya zo kan sahabbansa su koma madina, All..ya wajabta masu komawa madina.
Sannan mun yi maganar abinda ya sa All..T ya Zabawa Manzon All..(s) Madina a matsayin wurin hijira, a matsayin cibiyar kafa daular musulunci ta farko.
Mun bayyana cewa, da farko Madina bai yin isa daga Makka sosai ba, don hanya ce ta mutanen Makka zuwa harkokin kasuwancinsu a kasar sham a ko wace shekara.
Kuma mutanen Madina sun hada da larabawa Mushrikai, wadanda sune suka fi yawa, sannan akwai larabawa yahudawa, wadanda su kabilu 8 ne, kuma saboda Yahudawan da suke rayuwa kusa da su ne yasa suka zama yahudawa, tunda su Ahlul kitabi ne, suna da littafin Attaura na annabi musa.
Yahudawan sun hada da Banu qainuqaa, Banu Nadhir da Banu Qaraidha. Sun fi kowa dadewa a Madina.
Mun bayyana cewa, tare da wannan kiran Manzon All..(s) za iyi sauki, tunda Mushrikam Madina da suka rake basu musulunta ba, sun saba da jin kalmomi na addini suna kuma fahintar ma’anansu. Wato, sun saba da jin All.., Lahira, Aljanna, Wuta, da sauransu daga yahudawan da suke tare da su. Don haka idan ya kirasu zuwa addinin musulunci zasu fi sauran Fahinta, idan an kwatantasu da mutanen Makka, wadanda basu saba da wadannan kalmomi ba.
Sannan daga karshen mun ce Manzon All..(s) yayi hijira zuwa Madina a ranar daya ga watan Rabi’ul Awwal, kuma yayi kwanaki 9 a hanya kafin ya isa wani Kauye da ake kira Quba a bayan Madina, inda ya zauna a nan nay an kwanaki yana jiran isowar Aliyu dan Abitalib (a) tare da iyalansa, wadanda suka hada da Fatima diyarsa da sauransu. Bayan isowarsu ne ya shiga Madina tare da su. Mun bayyana cewa Kabilun Khazraj da Aus ko wannensu yana son kusantar Manzon All..(s) da musulmi don samun karfi da su a kan abokin hamayyarsu, tunda sun dade suna yakar juna. Kuma sun rika yahudawan madina shiga addinin musulunci.
Wannan saboda sun sha ji daga wajensu kan cewa wani Manzon zai bayyana a tsakaninsu a Madina su yakesu da tare da shi, basu san cewa Manzon ba bayahude bane.
Manzon All..(s) tare da iyalan gidansa, sun shiga birnin Madina a ranar Jumma’a, banda ranar Jumma’a wacce ta sameshi a garin Quba, inda a camma, ya gina masallaci na farko ya kuma yi masu sallar Jumma’a ta farko a addinin musulunci.
A Randa ya shiga Madina kuma, ranar Jumma’a ce, ya shiga garin a dai dai lokacin azzarahar. Mutanen gari suka tarbeshi, suka yi maraba da shi. A sannan yayi masu sallar Jumma’a, inda a cikin khudubobinsa na sallar Jumma’a ya kirasu zuwa ga tsoron All..da kuma taqwa, da aikin alkhairi da kuma jihadi kan tafarkin All…
A lokacin sahabban Manzon All..(s) sun kasu kashi biyu ne, akwai muhajirun, wadanda suka kaura daga Makka, zuwa Madina, da kuma Ansar masu taimaka masu, wato mutanen Yathriba ko Madina. Tun daga lokacin kuma aka fara kiran garin da Madinan Manzon All..(s).
Da haka, kuma addinin musulunci da farko ya bayyana a Makka, na tsawon shekaru 13, amma daga karshe ya kafa daula a Madina inda Manzon All..(s) shi ne shugabanta, kuma shine yake da ikon fada a ji kuma a aiwatar da umurninsa a kan kome. Sannan a cikin madina mutane suna kara shigar addinin musulunci, a hankali a hankali.
Karuwar yawan musulmi da sauri a Madina ya bawa Manzon All..(s) damar samar da al-ummar musulmi ta farko, kuma mizanin samar da al-ummar musulmi a lokacin an gina su ne bisa al-amura guda ukku, da farko gina masallaci, wurin sallah da kuma taro na farko ga musulmi, inda Manzon All..(s) yake karantar da su addini, ya fada masu sabbin umurnin All..T, ya kuma nuna masu yanda ake bautar All..kamar yanda yake so. Na kuma kuma ya kulla yan’uwantaka tsakanin muhajirun da Ansara, saboda dauke muhajirun, bakonta da suke ciki, bayan da suka bar duk abinda suka mallaka suka yo hijira zuwa Madina.
Sai kuma abu na ukku, wanda shi ne samar da dokokin zamantakewa da sauran mutanen Madina wadanda ba musulmi ba, wato larabawa yahudawa, wadanda muka bayyana cewa su kabilu 8 a lokaci, da kuma yahudawan kansu.
Da farko Manzon All…(s) ya kawo karshen bambanci tsakanin larabawa na kabilanci na Jahiliya, ya bayyana masu musulmi yan’uwan juna ne, daga ko wace kabila ya fito. Ya maida addinin musulunci ne asasin dangantaka tsakanin mutane ba kabilarsu ko launin fatarsu kamar yadda yake a jahiliyya ba. Wato kafin bayyana musulunci. Duk wanda yace la’ilaha Illallah ya zama dan’uwa ga sauran musulmi.
Don haka mutum hatta, idan akwai dangantaka ta jini tsakaninsu, wannan dangantakar ta yi Rauni, dangantakar su ta addinin ta fi karfi, kuma itace ta farko. Hatta idan mutum yana da kabila, dangantakarsa da kabilarsa ta yi Rauni, ta addinin ce tafi karfi.
Daga nan muna iya cewa, tun kwanaki na farko da yin hijira, Manzon All..(s) ya fara gina al-adu da ci gaban addinin musulunci a cikin sahabbansa, muhajirun da Ansar. Har’ila yau tsarin shugabanci na farko a musulunci, wanda Manzon All..(s) ya bawa sahabbansa labarin tabbatar haka, a sabon addinin musulunci y afara tabbata