Al-Adu Da Ci Gaban Musulunci A Tarihi 02

02-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da saduwa a cikin shirimmu na ‘al-adu da ci gaban musulunci’ wanda ni Tahir Amin zan ci

02-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da saduwa a cikin shirimmu na ‘al-adu da ci gaban musulunci’ wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a wani wani mako sau guda daga sashen hausa na muryar Jumhuriyar musulunci.  Da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu na yagabata mun bayyana manufar wannan shirin da kuma abunda muke son masu sauraro su fahinta a cikinsa. Mun bayyana cewa, addinin musulunci ya bayyana a dai dai lokacinda dan’adam yakedab da halaka saboda rashin shiriya. Don haka addinin musulunci ya zowa larabawa a dai dai lokacinda suka kasance cikin matukar bukatar shiriya.

Kuma don irin karfinda addinin yazo da shi a cikin shekaru 23 kacal ta yadu cikin kasashen larabawa, sannan kafin shekaru hamsin da bayyanarsa ya sami iko da mafi yawan kasashe masu muhimmanci a duniya. Ta kuma zama daula wacce babu irinta a duniya.

Musulunci ya ci gaba da iko da mafi yawakasashen duniya yana kuma yada al-adunsa wadanda suke kawo ci gaba a kowani bangare na rayuwar bil’adama. Wannan duk da cewa ya yi ta gamuwa da matsaloli nan da can a cikin shekaru 1400 da suka gabata.

Amma hakan bai hanashi ci gaba ba. Mun kuma bayyana cewa a cikin yan karnukan da suka gabata, musamman bayan yakin duniya na daya da kuma mamayar da kasashen yamma suka yiwa duniya, sun yi kokarin nuna cewa, al-adunsu ne kawai al-adu duk wanda bai tare da su ba wayayyu banae. Mun kuma yi maganar yadda suke daukar ci gaban da musulmi suka samu a baya a matsayin ci gabansu, sai dai su canza masa suna su bayyana cewa al-adarsu ne.

Da haka kuma suka bi kasashen duniya suna tilasta masu al-adunsu suna kuma musanta duk wata al-ada da ba tasu ba. Suna ganinsu al-adun ci baya.

Mun bayyana cewa addinin musulunci yana da dabi’ar shigar da wasu al-adu cikins idan hakan bai sabawa asalin addinin musulunci ba, don haka addinin musulunci yanadauke da al-adun wasu manya-manyan kasashe ko kabilun da suka ci gaba a duniya kafin bayyanarsa, wadanda suka hada da farisawa, misrawa da larabawa. Don haka sai ya zama babu addini ko ci gaban da yafi shi yalwa da fadi a cikin al-adun da kuma ci gaba.

Sannan daga karshe mun bayyana cewa akwai bukatar yara su san irin wahalar da iyayensu suka sha don raya wadan nan al-adu, don su san muhimmancinsu.

A yau zamu yi magana kan wasu al-amura masu muhimmanci wadanda addinin musulunci ke da su, wanda kuma ya taimaka wajen ci gabansa, daya daga cikinsu shi ne halaye masu kyau. Halaye masu kyau ya taka rawa wajen jawo hankalin da dama daga cikin wadanda ba musulmi ba shiga wannan addinin.

Wani masani Geage Zidan wani marubuce dan kasar Lebanon kuma kirista ya bayyana a cikin wasu daga cikin rubuce rubucensa yana cewa: Abu na farko wanda manzon Allah(s) yayi bayan hijirarsa daga Makka zuwa Madina shi ne hada yan’uwantaka tsakanin mutanen madina da wadanda suka yo hijira daga Makka zuwa madina suka kuma bar duk abinda suka mallaka.

Wannan yan uwantaka ya sanya, mutanen Madina suka dauki musulmi yanuwansu daga macce kamar yanuwansu na jina. Dankon zumuncin da wannan yanuwantaka ya haifar ya zama ginshikin da aka gina addinin musulunci a kansa. Wato kan cewa musulmi dan uwan musulmi ne a duk inda ya kasance a duniya.

Zeedan yana ganin gina addinin musulunci a kan wannan ginshiki na halaye masu kyau ya maida shi addinin wanda yayi imani da halaye masu kyau wanda ya kara dankon zumunci tsakanin musulmi. Insa zaka ga ba’ansare ya raba dukiyarsa biyu ya bawa dan’uwansa musulmi wanda yayi hijira, ba tare da yana ganin yayi asara ba. Ko kuma yana ganin yayi riba, don yana da yakini kan cewa Allah zai saka masa da abinda yafi haka a lahira. Wani lokacinda ma tun duniya zai fara ganin sakamakon hakan.

Addini da kuma halaye masu kyau suna tafiya tare, ba sa rabuwa da juna, duk wanda yake riya addini, to kuwa in gaskiya ne za’a ganshi a halayensa masu kyau.

Da dama daga cikin masana a wannan zamanin suna ganin, duk tare da ci gaba na kere keren na zamani a kasashen yamma, amma zaka ga cewa, ci gaban baya tafiya da halaye masu kyau. Ko kuma muna iya cewa, akasin haka al-amarin yake tafiya. Saboda zaka ga wadanda suka fi tara abinda duniya sun fi kowa lalacewa da kuma mummunan halaye.

Buchanan J Patrick wani marubi dan kasar Amurka ya bayyana a cikin littafinsa mai suna ‘Mutuwar Kasashen Yamma’ yana cewa, me yasa mutane a kasashen yamma a bangaren ilmi na duniya suna ci gaba amma cikin halaye masu kyau kuma suna rarrabe rarrabuwa mai kaiwa ga mutuwa?.

Masana da dama sun bayyana ra’ayinsu dangane da abinda ya sa hakan ya kasance, kuma suna ganin daya daga cikinsu, ya hada da cewa, a lokacinda kasashen yamma suka sanya mutum shi ne manufar kome, sun gina al-adunsu kan abubuwa ukku, na farko bukatun mutun shi abinda lura da farko kafin kome, sannan abinda suke kira yenci, da kuma yin watsi da addini.

Suna cewa a makarantar ‘humanism’ ko tunani mutum a matsayinsa shi kadai, an gina tunanin mutum a tunanin cewa, shi mutun yana da yencin yin abinda ya gaba dama, babu ruwansa da sama, wato babu ruwansa da addini, sannan baya bukatar shiriyar Ubangiji a rayuwarsa a duniya. Don haka bisa wannan tunanin, ci gaban kasashen yamma ya zama mutum yana tunanin kansa shi kadai da kuma yanda zai yi ya kaiga gurinsa shi kadai a cikin al-umma ne, don haka daga nan yayi watsi da abinda muke kira halaye masu kyau, inda mutun baya tunanin kansa shi kadai, kuma yana ganin wajibinsa ne ya tuna da wadanda suke rayuwa da shi ya kuma taimaka masu.

Wannan tunanin ba abinda ya haifar a kasashen yamma in banda, dauke halaye masu kyau a cikin jama’a da kuma maida su sakakku wadanda basa mutunta duk wani abu da kyautatawa wani. Sannan a cikin akidar watsi da addini kuma, sun zama mutane wadanda  ba ruwansu da addini a tsarin kafa dokoki,  wadanda suka gudanar da rayuwar jama’a ko kuma daddaikun mutane.

A yau wadan nan ginshikan da aka gina rayuwa a kasashen yamma, sun kama kasa, kuma su suka maida su kamar yadda suke, wato asalin bukatar mutum shi kai, da yenci wanda babu ruwansa da addini da kuma tsarin yin abinda yake so.

Wasu masana suna ganin wannan halin ya sanya ci gaban kasashen yamma, ya zama mai kin samuwar halaye masu kyau, a zamantakewar mutane, sai ya zama musiba a cikinsu. Wannan duk da cewa, magabata wadanda suka yi suna a baya suna kan wannan akidar da imani da halaye masu kyau, kuma a kansa suka gina rayuwarsu suka kai inda suka kai. Sai dai a halin yanzu ya zama abin ki a cikin mutane a kasashen yamma. Basa ganin addini face wani abu wanda magabata suka kirkiro don takaita mutum a matsayinsa na mai kwakwalwa kuma mai wayo wanda yake iya magancewa kansa duk wata matsala da ta bullo a gabansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted