Al-Adu Da Ci Gaban Musulunci A Tarihi 05

05-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci a cikin tarihi’ shiri wanda

05-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci a cikin tarihi’ shiri wanda yake kawo maku al-adu da ci gaban da addinin musulunci ya samu tun bayan bayyanarsa ya zuwa yanzu, wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasace tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…Masu, sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi magana rayuwar larabawa kafin bayyanar addinin musulunci, wanda zai bamu damar sanin irin mummunan halin da suke ciki sannan All..ya tsamosu daga halin da suke ciki ya basu shiriya mafi girma da ya taba bawa wani daga cikin halittunsa, wanda kuma shi ne addinin musulunci.

Mun kasa rayuwar larabawa kasha uku, akwai rayuwarsu tun zamanin Sabaa, da kuma Himyari, wandanda sune ake dangantasu da tarihin larabawa mafi dadewa, sai kuma zamanin Jahiliyya, wanda ya fara daga shigar shekaru 600 da haihuwar annabi Isa (a). wannan zamanin ya zo karshe bayan bayyanar addinin musulunci. Sai kuma daga bayyanar addinin musulunci har zuwa yau.

Mun bayyana cewa, tun lokacinda suka bar addinin annabi Ibrahim wanda ya gina dakin ka’aba rayuwarsu ta zama ta makiyaya wadanda suke neman duk inda ruwa yake don amfanin tabbobinsu, shi ya sa basu da manya manyan garuruwa, banda haka sun sharar da rera qasidu, harma ya zama mai girma a wajensu shi ne mai iya rare kasidu, inda ya yabi wani da wasida ya daukaka, idan kuma ya aibata wani da kisida ya kaskanta. Suna tarurruka na rera qasidu a ko wace shekara, inda suke gwada karfin kasidu mawaka daga cikinsu. Sukan yaki takobi, zaki, damisa, jarunta, da sauransu. Sannan wani abu kadan zaisa su shiga yaki a tsakaninsu, yaki wanda babu iyaka.

Basa da tausaiya saboda irin yanayin mai kaushi da tsananin da suke rayuwa a cikinsa, daga karshe mun yi maganar cewa, basa mutunta mata kuma suna bisnesu da ransu, saboda su a wajensu, marasa karfi ne wadanda basa iya kare kansu ballantana su kare wani a cikin dungi. Har muka kawo aya ta inda All…Ya yi maganarsu a cikin al-kur’ani mai girma, yana cewa:

{Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki. Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana} Annahl 58-59.

A fili All..ya bayyana yadda suke yi da yayansu mata, idan an haifammasu, ko su bisneta da ranta ko su riketa da wulakanci. Manzon All..(s) ya bayyana a cikinsu a lokacinda suke cikin irin wannan jahilcin da ta’assubanci, da kuma ikidu na ci baya da sauransu.

All..Ta’ala ya aiko da manzonsa na karshe, don ya fitar da su daga dohun jahilci zuwa hasken addinin musulunci, ya kuma aiko shi ga duniya gaba daya, saboda dukkan duniya su amfana da shiriyarsa, da kuma manzon da ya aika don shiryatar da su.

Wannan duk da cewa, idan ka kwatanta larabawan jahiliyya, da duniyar lokacin zaka ga cewa ba ta’inda zaka kwatantasu, saboda tsananin rayuwa a cikin kasashen larabawan ne ya sa, manya manyan kasashen duniya a lokacin suka kasa mamayarsu, basa kuma jin tsoronsu.

Amma bayan bayyanrsa(s), a cikin dan karamin lokaci, wanda bai fi shekaru 23 ba, ya samarda sauyi ta akidu, al-adu, zamantakewa da sauransu, wanda ba’a taba ganin irinsa a tarihin bil’adama ba.

Manzon All..(s) bayan bayyanarsa da shekaru 13 a Makka, ya koya masu ginshikan aqidu a addinin musulunci. Sannan bayan haka, akwai bukatar ya kafa gwamnati ko daula wacce a cikinta zai dabbaka akidun musulunci a aikata, sannan yanayin zamantakewa a Makka bai dace da kafa daula a cikinta a lokacin ba, don haka ya bukaci yin hijira daga Makka zuwa Madina, inda ya kafa daula wacce ta kunshi mafi yawan kabilun larabawa da kuma na wasu kasashen duniya a lokacin, inda ya tabbatar da akidar musulunci ta zama na kabilun duniya gaba daya.

A Makka, sukan bada matsayi ne a cikin al-umma tare da la’akari da kabilu da kuma matsayin da suke daukan mutum, a cikin su. Basa bawa wani matsayi bisa cancanta, sai dai bisa kabila da kakanninsa da matsayin iyayensa ko shekarunsa.

Amma a lokacinda ya koma madina, wannan tsarin ya sauya, saboda yakan dora bawa, ko dan bawa kan manya- manyan kuraishawa, kamar yadda ya bawa Usama dan Zaidu dan Haritha dan shekara 17 a duniya, mukamin kwamandan sojojin musulmi, zuwa yakar sojojin Roma, ya dorashi kan manya manyan kuraishawa muhajiruna da Ansar, kamar Khalifa na farko na biyu da na uku, saboda ya cancanci hakan.

Amma tunda akwai sauran tunanin jahiliya a cikin wasu daga cikin sahabban sa (s) a lokacinda wasu, duk da cewa sun san matsayinsa sun yi masa inkari. Sannan ya sanya bakar fata, kuma tsohon bawa a matsayin wanda yake kira zuwa ga abida mafi girma a addinin musulunci wato Sallah. A lokacin sallah, sai anji muryar Bilal dan Rabah(r) yana kira zuwa ga sallah.

Don haka saboda wadan nan dalilai da wasu Makka bai dace da kafa daular musulunci ta farko ba.

Wannan duk da cewa birnin Makka tana daga cikin birane, masu girma a kasashen larabawa, amma saboda wadannan dalilai bai cancanci ya zama cibiyar daular musulunci ta farko ba.

Amma banda abubuwan da muka ambata, akwai wasu al-amura wadanda suka bambanta Makka da Madina, suka kuma sanya madina ta fi dacewa ta zama cibiyar daular musulunci ta farko a kan Makka, duk da cewa annabin (s) daga can ya bayyana.

Daga ciki, akwai batun samuwar dakin All..T, dakin Kaaba a kusa da mutanen Makka, wanda yake basu nutsuwa, amma kuma sun garwata wannan dakin All..T da abubuwan shirka, gumaka, kuma sun hada kansu suna kare kasarsu don ta ci gaba da kasancewa kamar yadda iyayensu da kakanninsu suke so. Sun hada kai don ci gaba da jahiliya a cikinsa. 

Har’ila yau wani bambanci tsakanin Makka da Madina, shi ne, Mutanen Makka, yan kasuwa ne, zuwa sham kasar Yemen a cikin lokacin sanya, da kuma Sham a lokacin zafi, amma mutanen Madina manoma ne, suna noman abinda suke ci na dabino da sauran kayakin abinci, har’ila yau da kuma kiwon dibbobi masu yawa.

Wannan da kuma wasu dalilan sun taimaka wajen zaben da manzon All..(s) yayi wa Madina ya zama cibiyar gwamnatin musulunci na farko.

Kafin haka, manzon All…(s) ya je garin Ta’ifa, wanda bai da nisa daga Makka sosai, idan na kwatanta da Madina, amma irin halin da mutanen Ta’ifa suka karbeshi, ya sa ba zai yi garin ya zama cibiyar gwamnati, ko kuma wajen hijirar manzon All..(s) a cikin kasashen larabawa ba.

Don haka daga karshe, bayan bai’ar Aqaba ta biyu, da mutanen Madina ya fara tura musulmi zuwa Madina, saboda har’ila yau irin mutanen da suke zama a Madina, sun taimaka a dacewar Madina da zama wurin hijiransa (s) Kuma cibiyar daular Musulunci na farko. Sannan daga karshe, All..T ya sauko da ayoyi wadanda suka wajabta yin hijira daga Makka zuwa Madina ga Musulmi a lokacin, matukar suna da damar yin hakan.

Idan mun karanta tarihi zamu ga cewa, da dama daga cikin wadanda suka musulunta a Makka, basu sami damar yin hijira ba, saboda danginsu ko idan su bayi ne, wadanda suke mallakesu sun hana su yi hijira.

Bayan da, da dama daga cikin musulmi sun yo hijira zuwa Madina, Manzon All..(s) yayi hijira daga Makka zuwa Madina, ya kuma isa gewayen madina, wato Kuba a ranar litinin 12 ga watan Rabi’ul Awwal shekara ta 14 bayan fara manzanci. Ko kuma shekara ta farko bayan hijira. Da haka kuma aka fara tarihin musulunci tare da hijirar manzon All..(s) daga Makka zuwa Madina.

Manzon All..(s) ya dauki kwanaki 9  cur yana hijira daga Makka zuwa Madina. Sannan a cikin dan karamin lokacinda ya zauna a Quba, ya gina masallaci na farko a Musulunci.

Manzon All..(s) ya zauna a Quba nay an kwanaki ne, saboda yana jiran Aliyu dan Abitalib (a), ya karaso daga Makka zuwa Madina tare da iyalan gidansa. Sannan suka shiga Madina tare.

Idan kuma, muka dubi irin mutanen da suke zaune a cikin Madina a lokacinda musulmi suka yo hijira daga Makka zuwa can, zamu ga cewa akwai wasu kabilun yahudawa da suka rika kawo zuwa garin, sannan wasu manya manyan kabilun larabawa guda biyu, wato Aus da Hazraj.

Wannan ya sa da sauki mutanen madina zasu iya amincewa da wani sabon addini a tsakaninsu, tunda dama ba addinin daya suke da shi ba. Sannan larabawa wadanda basa bin addinin yahudanci a lokacin ma, (tunda akwai wasu kabilun larabawan wadanda suke bin addinin yahudanci, su 8 ne)- don haka ko larabawa wadanda ba yahudawa ba, (wadanda su suka fi yawa)  sun saba da jin akidun addini wadanda suka hada da All.., wahayi, Lahira, Aljanna, wuta da sauransu. Don haka da sauki suna iya fahintar addinin musulunci. 

Wannan ma wani kari ne daga cikin muhimmancin Madina, ko Yathriba a lokacin wajen zama cibiyar daular Musulunci ta farko.

Sannan wani abu mai muhimmanci, a nan shi ne, kabilun Khazraj da kuma Aus, wadanda sune suka fi yawa a Madina, idan an kwanatatasu da sauran kabilun, ko larabawa yahudawa, ko kuma yahudawa zalla, sun dade suna yaki a tsakaninsu, don haka shigowar manzon All..(s) Madina, ya sa ko wanne daga cikin wadan nan kabilu suna kokarin kusantar manzon All..(s) da kuma musulmi don samun mataimaki kan dayan bangare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted