Lebanon: Kakakin Majalisar Dokoki ya yi watsi da yarjejeniyar sulhu da Isra’ila

Kakakin Majalisar Dokoki ta Lebanon Nabih Berri ya yi watsida yarjejeniyar zaman lafiya da AMurka ta shiga tsakani aka cimma da gwamnatin Lebanon yana mai

Kakakin Majalisar Dokoki ta Lebanon Nabih Berri ya yi watsida yarjejeniyar zaman lafiya da AMurka ta shiga tsakani aka cimma da gwamnatin Lebanon yana mai shan alwashin jagorantar ‘yan adawar siyasa na kasar akan su ki amincewa da ita a Majalisar Dokoki.

Mista Berri ya bukaci Firaminista Nawaf Salam da ya janye daftarin yarjejeniyar mai cike da ce-ce-ku-ce.

Ya yi gargadi game da yarjejeniyar da ya bayyana a matsayin wacce za ta iya haifar da rikicin gida a kasar ta Lebanon.

Ƙungiyar Amal, wacce ke karkashin jagorancin Nabih Berri, ta kuma yi watsi da yarjejeniyar, tana mai jayayya cewa yawancin tanade-tanaden ta sun wargaza muradun kasar Lebanon akan na gwamnatin Isra’ila.

Shi ma Babban jami’in majalisar dokokin Hizbullah, Hassan Fadlallah, shi ya yi Allah wadai da yarjejeniyar da aka cimma a karkashin sulhun Amurka, yana mai kiranta “cin zarafi,” da abun”kunya,” da kuma mika wuya.

Furicin na su ya zo ne a daidai lokacin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci sojojin Isra’ila a kudancin Lebanon a ranar Talata, yana mai bayyana cewa sojojin kasar za su ci gaba da kasancewa a yankin.

Duk da tsagaita wuta, gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan wuraren zama da kayayyakin more rayuwa na fararen hula a duk faɗin kudancin Lebanon.

Tun daga ranar 2 ga Maris, Isra’ila ta kaddamar ke kai hare-hare a Lebanon, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 4,247, tare da jikkata sama da 12,190, da kuma sama da wasu miliyan 1.6 da suka rasa matsugunansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted