03-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci’ shiri wanda yake kawo maku al-adu da ci gaban da addinin musulunci ya samu tun bayyanarsa ya zuwa yanzu, wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasace tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…Masu, sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi magana kan yadda kasashen yamma, bayan sun shimfida ikonsu a kan kasashen duniya da dama sun fara gabatar da al-adunsu a matsayin al-adu na ci gaba da wayewa, sannan sauran ci gaban da wasu al-ummu suka samu ba ci gaba bane.
Sannan mun bayyana cewa a cikin gaban kasashen yammu sun gina akidunsu ne kan ‘dan’adm da kuma abinda zai iya yiwa kansa, sun ce basa bukatar addini, basa bukatar taimakon sama don rayuwa a duniya, wannan duk da cewa a zahiri suna daukar kansu kiristoci ne, amma a aikace ba ruwansu da addini.
Sanna mun bayyana halin yan’uwantaka wanda manzon Allah (s) ya shuka a cikin musulmi bayan hijirarsa daga Makka zuwa madina, inda ya kulla yan’uwantaka tsakanin muhajirun da Ansar wanda ya nuna yadda addinin musulunci ya himmatu da aiki tare da taimakawa juna tsakanin musulmi.
Wannan halin na yan’uwantaka, ya wanda babu irinsa a cikin wasu addinin ko kuma wayewar al-ummun da suka gabata ya kafa asasin halaye masu kyau a cikin addinin. Kuma ba wanda zai yi Imani da shi sai wanda ya yarada akwai lahira, tunda yanuwanda wanda manzon Allah (s) ya kulla tsakanin sahabbansa Ansar da muhajirun, ya kaiga mutumin Ansar zai raba dukiyarsa biyu ya bawa dan’uwansa muhajir wanda yayi hijira raba ya dauki rabi. Kuma wannan bai tsaya nan ba, a cikin lokacin yan uwantakar duk wata matsala wanda dan’uwanda muhajir ya shiga zai taimaka masa.
Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda aya ta zo ta shafin hukuncin yan’uwantaka ta farko.
Munji yanda wasu masana daga kasashen yamma suka tabbatar da hakan, suka bayyana cewa, wannan halin na yan’uwantaka wani babban al-amari ne a musulunci. Wasu daga cikin masana na kasashen yamma sun bayyana cewa irin halayen da mutanen kasashen yamma suke rayuwa a cikinsa ba rayuwar da yakamata dan’adam ya tafi kansa ba. Saboda abinda suka gani kan cewa lallai za’a kai wani lokaci wanda irin wannan rayuwar ba zai taba ci gaba ba.
Suka ce, wannan rayuwa wacce take sabani da Imani da lahira, da kuma abubuwan da suka shafi Imani ba zai ci gaba ba, tunda hatta iyayensu kafin wannan zamanin sun yi Imani da samuwar mahalicce da samuwar wata rayuwa bayan wannan rayuwa.
Atakaice rayuwa da ci gaban kasashen yamma, sun yi hannun riga da samuwar ubangiji wanda dabi’ace a rayuwar mutum, ko yarda ko kuma yake yarda. Wasu sun kara da cewa wannan rayuwa ta rashin Imani da addini, wanda kasashen yamma suke ciki, ya zama musabbabin faduwar wayewa da ci gaban kasashen a halin da ake ciki.
Buchanan J Patrick, ya kawo a cikin littafinsa mutuwar kasashen yamma yana cewa: A shekara 1983 a dai dai lokacinda ake maganar karancin likitoci a kasar, mutane 600 ne suka a kasar sanadiyyar cutar AIDS, wanda ya nuna cewa dabi’at ta sakawa masu auren jinsi guda wadanda wadanda suka yi tawaye wa dabiar da aka halcci mutum cikinsa.
Da dama daga cikin wadanda suka kamu da cutar HIV-AIDS basa iya rayuwa sai da tarin magungunan da suke sha a ko wace rana. Wannan duk sakamakon rashin amini da sabuwar mahacci ko kuma addini ne ya jawo hakan.
Banda hakan halaye na auren jinsi guda, wanda baya bawa mutane damar haihuwa yana nufin share samuwar mutum daga doron kasa ne.
Zubar da ciki, yawan sakin aure, raguwar yawan haihuwa, yawaitar kashe kai tsakanin matasa, shan kyayoyi masu sa maye, tozarta mata da wulakanta tsoffi, yin abinda aka ga dama tsakanin mata da maza, da wasu abubuwa da dama, duk suna nuni ne ga karshen ci gaban kasashen yamma.
Murubucin ya kara da cewa, tasirin al-adu da ci gaban kasashen yamma ya na kama da shan heroine ne, da farko zai sa mutum samun nutsuwa amma idan ya dade zai kashe shi.
Har’ila yau Kenneth Minog, wani marubuci ba’amerike a cikin littafinsa mai suna ‘sabon mizani’ yana cewa, saboda haka, ba zamu fitita ci gaban kasashen Turai da Amurka kan ci gaba wasu al-ummu ba, saboda yin watsi da wadannan halaye masu kyau.
Bisa abinda ya tabbata a cikin ko wace al-umma ko jama’a shi ne, kiyaye halaye masu kyau, da mutunta abubuwan da suka shafi addini, kuma mutane suka kiya halaye masu kyau, fadin gaskiya, barin karya da taimakawa raunana, kiyaye adalci, da sauransu, sune suka tabbatar da wanzuwan wannan al-ummar.
Dr Vilati, marubucin littafin “Ci gaban al-adun musulunci da kuma kasar Iran” yace: Idan wani ci gaba ya kai matsayinda, mutane sun daina mutunta dokoki, wannan ci gaban zai yi rauni, sannan daga karshe zai kai ga rashin tsaro a cikinta, da kuma rashin tsari, daga nan al-ummar zata fara rasa rukunan ci gabanta, har kuma ta fadi gaba daya.
Da wannan dalilin ne aka gina ci gaban addinin musulunci kan halaye masu kyau, tunanin samuwar Ubangiji da neman kusanci da shi, hadin kai, kula da dukoki, da kuma ka’idojin zamantakewa, na daddaikun mutane da al-umma.
Masana suna ganin al-amura da suka shafi rayuwar bil’adama, suna da wuce gona da iri ko kuma gazawa a wasu lokutan. Suna ganin wadan nan al-amura suna wuce wadannan marhaloli daya bayan daya, tare da wadannan kurare kuran. Amma samuwar wadanan halaye masu kyau da muka ambata da kuma amini da addinin suna taimakawa duk wata al-ada ko ci gaba, wajen yaduwa da kuma hanasu wargajewa kwata-kwata.
Haka al-amarin yake, idan wasu al-adu da ci gaba sun sami kansu ba tare da kula da wadannan halaye masu kyau da kuma Imani ba, ko da da farko sun sami nasarar yaduwa, amma ba za’a dade ba sai kaga sun rushe.
Masana sun bada misali da rushewar daular musulunci a kasar Andulos ko Espania a halin yanzu, duk sun nuna cewa shuwagabannin musulmu da sauran mutane, sun yi nesa da halaye masu kyau, sun karkata da koyawar addinin musulunci, wanda ya kaisu ga rushewa da kuma mamayar kasar da kuma korar musulmi daga kasar kwata-kwata.
Addinin musulunci ya kodaitar ya kuma karfafawa musulmi na kiyaye halaye masu kyau a tsakaninsu, su yi riko da imaninsi da All..da yin ayyukan saboda shi, rashin haka zai jawo masu matsaloli da dama.
Malamai sun bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sanya manzon All..(s) da sahabbansa suka yo hijira daga Makka zuwa madina shi ne su kaucewa mummunan halayen da mutanen Makka suke rayuwa a cikinsa, amma a madina su kadaine, don haka su da yaransu zasu iya dabbaka dukkan halaye masu kyau wadanda manzon All..(s) ya koya masu. Hakama yaransu zasu tashi cikin tarbiyyar addinin musulunci masu gyaran halin mutane.
All..ya wajabtawa musulmi yin hijira daga Makka zuwa madina a lokacin, har zuwa lokacinda musulunci ya sami nasara a kan kurasihawa, halaye masu kyau suka zama abin koyarwa a cikin birnin, sai aka dauke haramcin.
Har’ila yau wani abu da ke iya rusa ci gaba a ko wace al-umma akwai jahilci da kuma shugabancin kama karya. Will Durant, wani masanin tarihi ba’amurke yana cewa wulakanta ilmi da kuma watsi da shi yana daga cikin al-amuran da zasu iya rusa ci gaban da wata al-umma ta samu.
Hakama Ibn Khaldun, shi ma sanennen malamin addini, ya ce, shugabancin kama karya, da zalunci mai yawa yana iya kawo karshen duk wani ci gaban wa wata al-umma ta samu.
Sai kuma kuma rashin hadin kai, wanda yake samuwa saboda nuna bambanci da fifiko tsakanin musulmi. Tun bayan da manzon All..(s) ya kafa daular musulunci a Madina, ya samar da mafi kyawun halaye a tsakaninsu, yana barin duniya al-amura suka fara sauyawa. Sannan a lokacinda Banu umayya suka yi watsi da wadan nan halaye, suka kaskanta wadanda ba larabawa ba, cikin musulmi al-amura suka fara sukurkuce maya har sai da ya kai ga faduwar daularsu a hannun farisawa.
Sai kuma rayuwar al-mubazzaranci da kawace-kawace, musamman a wajen shuwagabanni da masu hali, a dai dai lokacinda talaka yake cikin mawuyacin hali, wannan ma yana gaggauta wargaza al-umma. Muna da kekyawar misala a daular banu umayya, a sham da kuma Andulus. A lokacinda suka shagaltu da kansu suka kyale talakawa sai All..ya turu abumuslimul Khurasani daga kasar Farisa ya zo ya zubar da daularsu. A kasar Andulos kuma turawa suka farmasu da yaki, suka sami nasara a kansu.
Sannan akwai kuma dalilali na farmakin makiya daga wajen daular, kamar yadda mongolawa suka farwa daular Abbasiyawa suka kawo karshensu, da yakin salibiyya, wadanda kiristoci suka kawowa musulmi suka kwace birnin Qudus.
A shirimmu nag aba zamu ga irin kokarin da musulmi suka yi na kiyake al-adu da ci gaban musulunci tun bayyanarsa.