07-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci a cikin tarihi’ shiri wanda yake kawo maku al-adu da ci gaban da addinin musulunci ya samu tun bayan bayyanarsa ya zuwa yanzu, wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasace tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…Masu, sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi magana dangane da yadda manzon All..(s) ya kafa daular musulunci ta farko a Madina, mun kuma bayyana dalilan da suka sa manzon All..(s) ya zama madina ya zama daular musulunci ta farko. Inda muka ambaci garin ya dace da zama daular musulunci ta farko, ta bangarori dadama daga cikin ta irin mutanen da sukezama a Madina, wadanda suka hada da Labarawa yahudawa, kabilun yahudawa guda uku, da kuma larabawa Mushrikai.
Wannan ya sa, larabawa Mushrikai wadanda suka fi yawa a garin sun saba jin kalmomi na addini kamar All.., Aljanna, wuta, Lahira dasauransu. Don haka manzon All..(s) ba zai sha wahala wajen bayyana masu addinin musulunci ba.
Mun bayyana cewa manzon All..(s) a Madina shugaba ne shi ne yake yanke al-amura na yaki da zaman lafiya shi ne alkali, kuma shi ne makamar dukkan al-amura a yankin.
Munji yanda manzon All..(s) ya samar da kundin tsarin zamantakewa na farko a Musulunci bayan ya karbi iko da shugabancin Madina, wato ya samar da al-umma wacce ta hada dukkan kabilu da addinai da suke madina.
Yahudawa masu bautar gumaka da kuma musulmi, su dimma, muhajirun daga kabilun Hazraj da Aus da kuma kurasihawa. Sannan kabilun Hazraj da Aus da yahudawa da Mushrikai duk sun zama yan’uwa idan sun zama musulmi, sannan wadanda ba musulmi ba zasu taimakawa musulmi masu iko da garin don tabbatar da zaman lafiya. Mun kuma tabbatar da cewa irin wannan daular ba’a taba samun irinta ba a tarihin bil’adama.
Wani kekyawar misali na tsarin musulunci mai kayatarwa shi ne, a zamaninda Imam Ali (a) ya karbi ragamar shugabancin al-ummar musulmi, ya kai karar wani bayahude a gaban al-kalin da shi ya nada, yana cewa garkuwan da ke hannun bayahuden nashi ne, sai Al-kali Shurai ya tsaida su a wuri guda sai y ace masa, shin kana da shaida ne, sai Imam (a) ya ce, babu:
Sai shuraih yace ai kuma magana ta kare na, yanke hukuncin garkuwan na wanda yake hannunsa na, don duk mai kara sai ya kawo shaida, don haka tunda baka dashaida, magana ta kare.
Sai suka tashi suka fita. Sai ba yahuden nan yayi mamaki ta yaya khalifan musulmi zai kai karar wani amma saboda bai da shaida a hanashi hakkinsa. Sai ya koma gaban al-kali ya ce: Ai garkuwa tashi ce, ba tawa bace. Sai shuraih Alkali ya kira amirulmumina (a) ya bashi garkuwansa sai kuma ya ce ya bawa bayahuden kyautarta don ta fada gaskiya.
Wannan shi ne musulunci wanda yake dai daita shugaba da talaka, ya kuma bawa talaka gaskiya, idan shugaban ya kasa tabbatar da gaskiyarsa.
Har’ila yau wani al-amuri mai muhimmanci wanda manzon All..(s) yayi bayan hijira, kamar yanda muka fada a shirye shiryemmu na baya shi ne gina masallaci, wanda ya maida shi cibiyar gudanar da sabuwar daular musulunci da ya kafa, hakaki masallaci a daular musulunci ta farko wurin ibada ne sannan cibiyar gudanar da harkokin daular ce. Kuma wurin warware matsaloli na sharia a ne a tsakanin al-ummar musulmi.
Banda haka masallaci makaranta ce inda manzon All…(s) yake karantar da su adddini, ya fada masu, sabbin umurnin All..da ya da aka saukar masa a cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma yayi masu bayanin umurnin All..T.
Banda haka masallaci a lokacin baitul mali ne, na ajiyar kudaden al-umma, sannan wuri ne na hurrasda sojoji da kuma kodaitar da su zuwa yaki.
Muna iya cewa, masallaci a lokacin shi ne wari mafi muhimmanci a wajen Musulmi a madina, saboda dukkan al-amura masu muhimmanci a cikinsa ake gudanarwa kama daga al-amuran siyasa, zamantakewa.
Don haka masallaci shi ne cibiyar tabbatar da karfi da kuma al-amuran addinin musulunci a Madina a lokacin. Nan ne ake tarbiyantar da mumunai wadanda sune ginshikin tsaida wannan addinin, saboda sune suke bada rayukansu da dukiyoyinsu don ganin wannan addinin ya tsayu da kafafunta.
Daga ciki, a masallaci ne ake koyawa musulmi maza da mata addini, nan ne ake koya masu rubutu da karatu.
Amma bayan wasu shekaru, kuma bayan wafatin manzon All..(s) a hankali a hankali, an raba masallaci, aka gina kutuna cikin harabarsa ko kuma kusa da shi, haka ma makarantu da Jami’o’iin ilmi daban daban ana ginasu ne kusa da masallaci.
Amma tabbatar da akidun addinin musulunci, wadanda sune asalin sakon da manzon All..(s) ya fara zuwa da su, kuma a kansu ne aka gina sauran rassan addinin musulunci, wadan nan suna bukatar taimakon bangare siyasa, da bangaren gudanarwa, da kuma bangaren tsaro ko kuma karfin soje, don ganin sun tabbata sun kuma tsayu da kafafunsu.
Saboda muhimmancin wadan nan al-amura, manzon All..(s) ya na bukatar kafa hukumomi wadanda zasu kula da wadannan rassa na gwamnatin musulunci a Madina, don haka ya zabi ma’aikata wadanda suke da korewa a ko wanne daga cikin wadan nan bangarori, ya kuma dora masu nauyin kula da su.
Masila, ya shi ne, ya zabi wasu ya dora masu, nauyin tattara zakka, daga ko ina karkashin daular, a madina ko wajensa, wasu kuma ya dora masu aikin kula da al-amuran zamantakewa a madina da wajensa. Wasu kuma bangaren ilmantarwa da kuma tarbiyya.
Wasun kuma, ya basu ayyuka daban daban, wadanda suka hada da tsara takardun gwamnatin kamar al-kawulan da aka kulla da mutane da kabilu da kuma wasu kasashe, da rubuta lissafin kudaden da gwamnati take da sun a zakka ne ko ganimar yaki da sauransu. Wasun kuma suna rubuta ayoyin Al-kur’ani mai girma wadanda ake saukarwa manzon All..(s) daga lokaci zuwa lokaci.
Manzon All..(s) ya zabi wasu daga cikin sahabbansa, don rijista ko rubuta, filaye da fadinsu, da wuraren ruwa ko rijiyoyi wadanda manzon All..(s) yake yankawa wasu, ko kuma ya bayyana abinda za’a yi da su.
Wannan tsarin gudanar da harkokin gwamnati, sabon tsari ne a cikin kasashen larabawa. Musamman bada takardan shaidar mallakar filaye, da rijiyoyin ruwa, da kududdukai da magudanun ruwa da sauransu.
Har’ila yau a wani bangaren, manazon All..(s) ya tattara takardun Yarjeniyoyi na kabilu daban daban, wadanda suka hada da Yahudawa da kiristoci da wasu sarakuna da shuwagabannin kabilun larabawa da wadanda ba larabawa ba. Ya tattarasu bisa yanayi daban daban da ko wannensu yake da shi. Wannan ya bawa wasu mutane mamaki kan wannan sabon tsarin tafiyar da gwamnatin wanda addinin musulunci ko mu ce manzon All..(s) ya zo da shi.
Daga cikin yanda manzon All..(s) ya tsara yarjeniyar sulhun hudebiyya tare da mushrikan Makka a lokacin, abinda aka kawo cikin sulhun da kuma yanda manzon All..(s) ya amince da su, ya tada hankalin wasu sahabban, har suka nuna rashin amincewarsu da al-amura da dama a cikinsa.
Tarihi ya tabbatar da korewa cikin harkokin gudanarwan sabuwar gwamnatin musulunci karkashin kula na manzon All..(s) ya sami nasarori daya bayan daya, a cikin lokacin da ya gudanar da harkokin shugabanci na tsawon shekaru 10 a Madina.
Tare da harkokin gudanar da gwamnati, manzon All..(s) ya aika wasiku zuwa sarakuna da shuwagabannin kasashe makobta wadanda suka hada da Sarkin Farisa, sarki kaisar na Ruma, da shugaban kasar Masar, da hakimin Yemen, da sarkin Habasha, da sauransu.
Babbar magana da cikin wadan nan wasiku shi ne kiran wadan nan shuwagabannin kasashe zuwa ga addinin musulunci, da kuma amincewa da bautar All.shi kadai. Bisa mahangar mafi yawan masu rubutun tarihi da masu nazarinsa, suna ganin manzon All..(s) ya kawo irin salon diblomasiyyarsa da kuma tsarinsa na hulda da kasashen waje a cikin wasikun nasa.
Manzon All..(s) a cikin wadan nan wasikun, ya nuna irin tsarin da yake tafiyar da huldarsa da kasashen duniya daban daban, kowa da irin salo na musamman da yake bi don isar da sakon addinin musulunci gareshi. Kuma yakan gabatar da dilomasiyya da farko sannan yayi maganar yaki ko rikici daga baya. Kuma idan sahabbansa suka kama wasu a yake yaken da ya umrcesu, musamman wadanda ba’a taba kiransu zuwa addinin musulunci ba, yakan sake su.
Daga nan sai manzon All..(s) ya fara fadada daular musulunci, da kuma samarda zaman lafiya da aminci a kan iyakokin daular, ta hanyar yake yaken da shi kansa yake jagoranta ko yake aika sojojinsa tare da jagorancin wasu daga cikin sahabbansa. Ko kuma ta hanyar kullayarjenioyar zaman lafiya da da wadanda basu musulunta ba.
Wannan yana daga cikin shirinsa (s) na isar da sakon musulunci ga kasashen duniya a cikin kasashen larabawa ko wasu kasashen.