Iran ta bayyana cewa tana sanya ido sosai kan yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad da ta cimma da Amurka.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce Tehran za ta sa ido sosai kan yadda Amurka ke aiwatar da yarjejeniyar.
“ya kara da cewa za mu aiwatar da alkawuranmu ne kawai idan dayan bangaren wato Amurka ta mutunta na ta,” in ji Baghai a wani taron manema labarai a ranar Talata.
” Wadannan kalamai sun zo ne yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da nuna rashin fahimtar juna kan aiwatar da yarjejeniyar mai matakai 14 da aka sanya wa hannu a tsakiyar watan Yuni, wadda aka tsara don kawo karshen yakin zalunci Amurka da Isra’ila kan Iran da kuma dage shingen da Amurka ta yi tashoshin jiragen ruwa da kuma neman sakin kudaden Iran da aka rike a kasashen duniya.
Mista Baghai ya bayyana tsagaita wuta a Lebanon shi ne sahun gaba a matakan da yarjejeniyar ta kunsa kuma shi ne mataki na farko na jarraba Amurka idan zata iya cika alkawuranta na tilasta wa Isra’ila dakatar da yaki a Lebanon.
Da aka tambaye shi game da rahotannin yiwuwar ganawa tsakanin jami’an Iran da Amurka a Doha, Baghai ya musanta cewa an shirya irin wannan taron.
“Ba mu tsara wani taro da jami’an Amurka ba, a kowane mataki, a cikin kwanaki masu zuwa inji shi.