Al-Adu Da Ci Gaban Musulunci A Tarihi 04

04-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci’ shiri wanda yake kawo maku

04-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Al-adu da ci gaban Musulunci’ shiri wanda yake kawo maku al-adu da ci gaban da addinin musulunci ya samu tun bayyanarsa ya zuwa yanzu, wanda ni Tahir Amin zan ci gaba da kawo maku a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasace tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…Masu, sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi magana dangane da yadda halaye masu kyau wadanda addinin musulunci ya zo da su tun farko farkon bayyanarsa, ya zama ginshiki wanda aka gida addinin musulunci a kansu. Kuma su ne suka rika jawo hankalin wadanda ba musulmi ba zuwa shiga addinin musulunci a tsawo tarihin bayyanarsa.

Kuma mun kawo misalai da kuma shaidar haka, daga baki ko rubutun masana, daga kasashen yamma musamman Amurka don tabbatar da hakan.

Har’ila yau munyi maganar yadda rashin amini da addini ya lalata kasashen yamma, ya kuma kaisu ga halaka, saboda Imani da samuwar mahacci, wani abu ne wanda Uabangiji ya shuka shi a halttan ko wani mutum, saba masa sabawa hankali da kuma zuciyar mutum wanda yake tunatar da shi kan cewa akwai wanda ya halacceshi, kuma duniyar nan bata samar da kanta daga babu ba, dole ne akwai wanda ya halicce ba.

Mun yi maganar yadda cutar HIV-AIDS ta zama aya ga wadanda suke son sauya dabi’ar da Ubangiji ya halicci mutane wato masu auren jinci. Wannan halayen nasu ya kaiga bayyanar cuta wacce ta zama bata da magani, kuma wadanda suka rayu daga cikin wadanda suka kamu da wannan cutar zasu rayune kawai tare da shan taron magunguna a duk ranar All…

Amma a ci gaba da shirimmu nay au, kamar yadda kowa ya sani annawan All.. suna da wani matsayi wanda ba wanda zai maye gurbinsu a gina al-adu da kuma ci gaba a addini.

Ubangiji ya umurci annabawa su kira mutane zuwa ga gaskiya da kuma hakika, kuma manufar aiko da annabawa itace kara yawan sani da ilmin mutane da kuma wayewar bil’adama. Tarbiyyar mutum don ya kai ga amincewa da aiki da adalci da daidaito a cikin al-umma.

Ubangiji a cikin aya ta 36 na suratun Alnahal yana fada dangane da aiko da annabawa kamar haka.

{Hakika ! mun tada manzo a cikin ko wace al-umma, kan cewa ku bautawa All.. ku kuma yi watsi da Tagutu… } 36 Annahal.  A garin Makka mai tsarki All..ya sha tada manay manyan annabawa. Kuma tarihi ya tabbatar mana kan cewa, bayan bayyanar annabi Ibrahim (a)-gwazon kadaita All..ko tauhidi- larabawa da dama sun shiga addinin tauhidi, wato kadaita All… Amma abin bakin ciki wasu daga cikin mabiyansa a bayansa, sun karkatar da addinin tauhi zuwa bautar gumaka, sun gurbata addinin tauhidin da ya bar masu da sharka ko kuma tarayyar da All…

Bisa abinda muka karanta a tarihi, zamu fahinci cewa, tun bayan wafatin annabi Ibrahim (a), har zuwa lokacin bayyana addinin musulunci, addinin larabawa yana garwaye tsakanin, bautar All..kamar mutunta aikin hajji, girmama dakin Kaaba, da tawafinsa da kuma bautar gumaka a lokaci guda.

Wannan duk da cewa ana samun wasu daddaikun mutane a cikin larabawan wadanda basa bautar gumaka, banda haka suna hana masu bautar gumaka bautarsu. Mutane kamar Abdul-Muttalib (kakan manzon All..) baya bautan gumaka.

Don karin bayani, zamu sake daba tarihin larabawa kafin bayyanar addinin musulunci. Malaman tarihi sun bayyana cewa, tarihin larabawa ya kasu kashi uku ne.

Akwai zamanin Sabaa, da kuma Himyari, wandanda sune ake dangantasu da tarihin larabawa mafi dadewa, sai kuma zamanin Jahiliyya, wanda ya fara daga shigar shekaru 600 da haihuwar annabi Isa (a). wannan zamanin ya zo karshe bayan bayyanar addinin musulunci. Sai kuma daga bayyanar addinin musulunci har zuwa yau.

A wani kason kuma malaman tarihi sun sake raba tarihin larabawa da yanayin yankin da kuma kabilunsu. A wannan rabon sun ce akwai Larabawa ‘Qahtani, da kuma Adnani, ko kuma mazauna garuruwa da kuma larabawan daji masu zama a kauyuka.

Don haka Larabawa ma, kamar sauran kabilu ne a duniya, akwai mazauna garuruwa da birane, akwai kuma kauyawa. Wannan halin haka yake a cikin sauran manya manyan kabilu a duniya, kamar Iraniyawa, Misrawa, turawa da Indiyawa.

Larabawa kafin bayyanar addinin musulunci, sun shahara da rera qasidu, da kuma koyon adabin harshensu. Kuma suna al-fakhari da hakan. Don haka zababbu daga cikinsu sune wadanda suka kware a tsara qasidu da iya magana.

Larabawa, musamman na kauyuka, sukan yi halka ko da’ira kewaye da irin wadan nan kwararru a ko yaushe suna sauraron sabbin qasisu da maganganu na hikima daga wajensu. Hakan yakan kayatar da su kuma yana basu nishadi.

Kasuwanni a kasashen larabawa a lokacin, kamar kasuwar Ukaza, wurare ne na gabatar da sabbin qasidu da kuma fasaha a cikin larabawa kafin bayyanar addinin musulunci a ko washe shekara.

Duk wata kabila wacce, kwarerren mawaki ya bayyana a cikinsu, sukan  yi alfakhari da shi sukan kuma shirya masa taron girmamawa a tsakaninsu.

Tasirin mawaka da masu rare qasida a lokacin jahiliyya ya kai ga, idan sun tsara wasida wacce a cikinta suka yabi wani mutum wanda ba kome ne a cikinsu, zai sami daukaka su kuma girmama shi, idan kuma ya rare qasida ya kaskanta wani babbam mustum a cikinsu, yakan kaskanta a cikinsu.

Wasu daga cikin qasidu wakokin da larabawa suke sha’awarsu, suke kuma sonsu kafin bayyanar addinin musulunci sun hada da, hamadar Hijaz, da Haimominta, sifanta takubba daban daban, da wasannin da suka saba yi a tsakaninsu, da halaye masu kyau a cikinsu da wasu al-adunsu masu kyau, kamar yawan kyauta, da sauransu, suna daga cikin abinda aka sani daga cikin tarihinsu.

A wannan bangaren na shirimmu zamu yi karin bayani dangane da zamani kafin bayyanar addinin musulunci a kasashen larabawa, zamanin da ake kira jahiliya, saboda al-amura na jahilci masu yawa da suke ciki a lokacin, da kuma aikata abubuwa masu nuna jahilcinsu dangane da rayuwa a nan duniyar, wani lokaci masu ban tsoro. Kamar bisne yaya mata da ransu, don a jahilcinsu, haihuwar macce a gida aibi ne don zata zama nauyi a kan dangin saboda ba zata iya yaki don kare dangin ba. 

Ko yaki kan abubuwan da basu kai sun kawo ba, na shekaru masu yawa, suna halaka kansu da kansu. Bandaka haka a lokacin babu wasu dokoki na zamantakewa, da ya shafi daddaikun mutane ko kuma na Jama’a, a kasashen larabawa. Duk wanda yafi wani ko wasu karfi shi ne shugaba.

Wani annabi bait aba bayyana a tsakaninsu ba, ballantana ya shiryar dasu da wahyin Ubangiji. Kuma ganin yadda mafi yawan kasashen larabawa a lokacin, musamman Hijaz hamada ce, busasshe, tare da rana mai tsanani, suna neman ruwa nan da can, a ko yaushe, wannan rayuwa mai tsanani yasa mafi yawansu sun rasa halayen yan’adamtaka wanda a wata dabi’a mutum bai kamata ya rasa su ba. Basa da tausayi ko kadan. Don yawace yawacensu, mafi yawansu ma zauna kauyuka ne. 

Saboda wannan, mafi yawan tarihin larabawa tarihin yake-yakensu ne, don haka suke kiran sa ‘ranakun larabwa’ wato yake yake don basu aikin da ya fi yaki. Zakaga wadannan yake-yake galibi, saboda sabani tsakanin kabilu kan dabbobinsu da wuraren kiwonsu. Kuma a cikin wadan nan yake yake ne suke farwa juna su yi wawason dukiyoyin junansu.

Sannan goyon bayan kabila ba tare da wani dalili ba, ya zama dabi’a a cikin larabawan jahiliya. Har aka ruwaito suna fadawa juna “ka taimakawa dan’uwa azzalumi ko wanda aka zalunta’. Don haka nuna kabilanci, ya zama dabi’a a cikin larabawa a zamanin jahiliyya, wanda ya maida su mutane wadanda basa son zaman lafiya, kuma suke cikin jayayya da yaki a ko yaushe.

Sukan tada yaki kan wani al-amari wanda bai kai ya kawo ba, su kuma dauki shekaru suka fafatawa a tsakaninsu.

Banda haka larabawa a jahiliyya, kafin bayyanar addinin musulunci, basa mutunta mata, basa ganinsu da wata daraja, suna daukarta a matsayin abin kunya da kaskanci. Don haka ne wasu lokutan sukan bisneta da ranta saboda haka. Larabawan jahiliya basa ganin mata sun cancanci gado, banda haka suna gadonta kamar yadda ake gadon kaya.

Alkur’ani mai girma ya kawo wannan batun a cikin ayoyin 58,59 a cikin Suratun Nahal. Yana cewa:

{Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki. Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana} Annahl 58-59.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted