Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi tattaunawa tahanyar wayar tarho da takwarorinsa na Indiya da Birtaniya
A yammacin jiya Juma’a, Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi tattaunawa ta hanyar wayar tarho daban-daban da takwarorinsa na Indiya da Birtaniya.
Ministan Harkokin Wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tattauna dangantakar kasashen biyu da ci gaban yankin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan Harkokin Wajen Indiya Subrahmanyam Jaishankar a ranar Juma’a da rana.
Araqchi ya kuma yi magana ta wayar tarho da Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya Ed Miliband, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma sabbin ci gaban yankin da na duniya.