Qalibaf: Amurka Ba Zata Yi Nasara A Yakin Tattalin Arziki Da Iran Ba

Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Amurka za ta gaza a yakin tattalin arziki da Iran Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin

Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Amurka za ta gaza a yakin tattalin arziki da Iran

Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake magana kan matsin tattalin arzikin da Amurka ke yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya yi ikirarin cewa: Amurka ta gaza a yakin soja da siyasa da ta yi da Iran, kuma za ta gaza a yakin tattalin arziki.

A lokacin ganawarsa da shugaban Majalisar Koli ta Shari’a ta Iraki, Qalibaf ya bayyana godiyarsa ga Iraki bisa gudanar da jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci, da kuma karbar bakwancin masu ziyarar Arba’een na Imam Husaini {a.s} a wannan shekarar.

Qalibaf ya bayyana cewa: Yana da matukar muhimmanci ga kasashen Musulmi su ajiye batutuwan da ke jawo ce-ce-ku-ce a gefe. Ya jaddada alaka mai zurfi tsakanin Iran da Iraki da kuma muhimmancin da suke da shi a halin da ake ciki a yanzu, yana mai cewa babu shakka Iran da Iraki za su iya taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin yankin, musamman a yankin Tekun Farisa.

A nasa bangaren, Fa’iq Zaidan Shugaban Majalisar Koli ta Shari’a ta Jamhuriyar Iraki ya yi nuni da sakon hadin kai daga al’ummar Iraki da gwamnatin Iran a lokacin yakin da ba a yi adalci ba, yana mai cewa, “Ina dauke da sakon hadin kai daga al’ummar Iraki da gwamnatin Iraki, kuma muna bayyana shirinmu na yin hadin gwiwa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted