Iran: Hadin Kan Musulmai Ne Zai Fitar Da Amurka Daga Yankin

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Samun haɗin kai tsakanin ƙasashen Musulmi yana share fagen ficewar Amurka daga yankin Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Samun haɗin kai tsakanin ƙasashen Musulmi yana share fagen ficewar Amurka daga yankin

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada wajibcin kafa kawance tsakanin kasashen Musumi domin karfafa zaman lafiya da tsaro a yankin, yana mai bayyana fatansa na samun hadin kai tsakanin wadannan kasashe zai share fagen ficewar Amurka daga yankin.

A ganawarsa da Fa’iq Zaidan, Shugaban Majalisar Koli ta Shari’a ta Jamhuriyar Iraki da tawagarsa da ke tare da shi, Masoud Pezeshkian ya yaba wa al’ummar Iraki da gwamnatin kasar bisa shirye-shiryen da suka yi na jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci mai cike da tarihi da kuma kyakkyawar tarbar da suka yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husseini {a.s}. Ya ce, “Yana matukar farin ciki da ziyarar tawagar Iraki zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma yana fatan wannan taron zai share fagen bunkasa da karfafa huldar al’adu, kasuwanci, da tattalin arziki tsakanin kasashenmu biyu.”

Da yake magana kan dimbin albarkatun da arzikin yankin, Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya suna kwadayin wadannan dukiya kuma suna neman haifar da takaddama, yaƙe-yaƙe, da rikice-rikice don su mamaye su, la’akari da cewa hanya daya tilo da za a iya tunkararsu ita ce a kula da hadin kan kasashen Musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted