Iran: Kwamandan Sojan Pakistan Ya Dauki  Sharuddanmu Zuwa Ga Washington

Kamfanin dillancin labarum "Tasnim" ya ambato wata majiyar gwamnatin Iran tana jaddada cewa an gabatarwa da masu shiga Tsakani na Paksitan sharuddan Iran akan batun
Asim Munir Na Pakistan A Fadar Shugaban Kasar Iran

Kamfanin dillancin labarum “Tasnim” ya ambato wata majiyar gwamnatin Iran tana jaddada cewa an gabatarwa da masu shiga Tsakani na Paksitan sharuddan Iran akan batun bude mashigar Hurmuz.

Majiyar ta ce daga cikin sharuddan da Iran ta gabatar da su na bude mashigar Ruwan Hurmuz da akwai komawa aiki da sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad,daga ciki har da bangare na biyar na yarjejeniyar fahimtar junan.

 A  Jiya Talata ne dai mataimakin shugaban kasarIran Allamah Mahdi Taba’taba’i ya bayyana cewa, sabanin yadda kafafen watsa labaru suke watsawa, ziyarar da shugaban sojojin kasar Pakasitan ya kawo zuwa Iran ta haifar da Da mai ido.

Taba’tabai ya kuma kara da cewa; Ziyarar Munir zuwa Iran wani cigaba ne ta fuskar diplomasiyya, kuma ba da jimawa ba za a ga sakamakon hakan a kasa.

A ranar Litinin ne dai kwamandan sojan kasar Pakistan tare da ministan harkokin cikin gida su ka kawo Ziyara Iran, inda  su ka gana da mahukunta kasar.

Daga cikin wadanda tawagar ta Pakistan ta gana da su da kawai babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Janar Muhsin Rizhai, wanda ya bayyana cewa; Ko Kadan Iran ba ta amince da Amurka ba. Don haka ya zama wajibi a gare ta ta sauya halayyarta domin aiwatar da yarjejeniyar.

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted