Kasashe 125 Ne A Duniya Suke Son Kama Benjamine Natenyahu

Kafar watsa labaru ta "Ziman Ysra'il" ta buga wani labari wanda ya kunshi bayanin alakar Haramtacciyar kasar Isra'ila da kasashen duniya, ta ce a halin
Natenyahu

Kafar watsa labaru ta “Ziman Ysra’il” ta buga wani labari wanda ya kunshi bayanin alakar Haramtacciyar kasar Isra’ila da kasashen duniya, ta ce a halin yanzu wannan alakar ta yi kasa fiye da kowane lokaci a tarihi.

Kafar watsa labarun ta kuma ce; Dalilin da ya jawo haka shi ne Yakin Gaza, da hare-haren Isra’ila a yammacin Kogin Jordan, da kuma yakin Iran.

Har ila yau kafar watsa labarun ta ambaci cewa tsoma bakin Netanyahu a cikin siyasar kasar Amurka yana daga cikin abinda ya jawo wannan koma baya.

Kafar watsa labarun ta kuma yi watsi da yadda Netanyahu yake riya cewa shi da Isra’ila suna da karbuwa ta musamman a duniya,domin abubuwan da suke faruwa a kasa sabanin haka ne.

Har ila yau kafar watsa labarun ya ambaci yadda kasashe 125 a duniya suke son kama Netanyahu da hana shi shiga cikinsu saboda hukuncin kotun manyan laifuka ta kasa da kasa.

A cikin watan Nuwmaba na 2024 ne dai kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo Fira Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila bisa zargin aikata manyan laifuka da su ka hada kisan kiyashi  akan al’ummar Falasdinu.

Dukkanin kasashen da suke mambobi a cikin yarjejeniyar Roma da ta kai ga kafuwar kotun, suna son ganin an kamo Netanyahu. Daga cikin kasashen da kawai na turai da su ka hada Faransa, Italiya, Jamus, Canada, Birtaniya da wasu kasashe da dama na turai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted