Tashar talabijin din Amurka ta ” NBC” ta watsa wani rahoto da ya kunshi yadda hare-haren Iran akan cibiyoyin leken asirin Amurka ya yi barna ta biliyoyin daloli.
Tashar ta NBC ta nakalto majiyoyi hudu da suke tabbatar da cewa hare-haren na Iran a kan cibiyoyin Leken asirin Amurka da tattara bayanai a wannan yankin sun rushe, ta yadda ba a baya yi wa cibiyoyin leken asirin Amurka wannan irin barna ba.
Majiyar ta kara da cewa; Barnar da Iran din ta yi wa kayan leken asirin Amurka ta biliyoyin daloli ce.
A halin da ake ciki a yanzu majalisar Amurka ta fara bincike da nazarin yadda za a sake gyara wadannan cibiyoyin Leken asirin da tattara bayanai.
Rahoton ya ce hare-haren Iran ba akan cibiyoyin soja kadai su ka tsaya ba, sun shafi cibiyoyin leken asiri.
Har ila yau rahoton tashar talabijin din ta Amurka “NBC” ya ce; Tun da aka kafa CIA a 1947 ba a taba yi mata barna irin wacce take fuskanta ba a wannan yakin.”
Iran dai ta sha jaddada cewa za ta kai wa cibiyoyin makiya hari a duk inda su ka buya a cikin wannan yankin.
Bugu da kari dakarun kare juyin juya halin musulunci sun ce; Daga yanzu duk wanda ya bai wa abokan gaba mafaka suna kawo wa Jamhuriyar musulunci ta Iran hari,to ya zama wanda ya yi tarayya da su a cikin yaki.