Bafalasdine guda ya yi shahada yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani tantin ‘yan gudun hijira a kudancin Gaza
Wani Bafalasdine ya yi shahada, sannan wasu sun jikkata a yau Laraba a wani harin sama da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani tanti ‘yan gudun hijira a garin Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza.
Majiyoyin yankin sun shaida wa manema labarai cewa: Harin ya yi sanadiyyar shahadar wani Bafalasdine da kuma jikkata wasu, wadanda aka mika su ga Asibitin Nasser Medical Complex don jinya. Wata majiya a asibitin Nasser Medical Complex ta tabbatar da isowar gawar mamacin da kuma wasu da suka jikkata bayan harin da jirgin saman yakin mamayar Isra’ila ya kai kan tanti.
Wannan ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka ayyana a ranar 10 ga Oktoban shekara ta 2015. Harin na sojojin mamayar Isra’ila ya kuma faru duk da kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na dakatar da kai hare-hare a Zirin Gaza.
A wata hira da ya yi da Fox News a ranar 17 ga Agusta, Trump ya bayyana cewa bai kamata Isra’ila ta kai hare-hare a Gaza ba, yana mai cewa Hamas ta amince ta kwace makamai a karkashin shirinsa na kawo karshen yakin a Zirin Gaza.