Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian tare da tawagarsa sun isa lardin Basra da ke kudancin kasar Iraki a yau Juma’a a rana ta uku ta ziyarar aiki da ya kai kasar Iraki da nufin duba ayyukan ci gaba da Iran din ke jagoranta a yankin.
A cewar karamin jakadan Iran a birnin Basra Ali Abadi, wannan ita ce ziyara ta farko da wani shugaban kasar Iran ya kai birnin Basra cikin shekaru 100 da suka gabata. Ana yaba wa ziyarar a matsayin wani lokaci mai tarihi na alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma nuna muhimmancin Iraki ga Iran.
Kafin ya isa birnin Basra, shugaba Pezeshkian ya ziyarci wasu lardunan Iraqi da dama da suka hada da Baghdad, Najaf, Karbala, Erbil, da Sulaymaniyah. Ziyarar tasa a birnin Basra ta kasance zangon karshe a rangadin da ya ke yi a kasar Iraki, wanda kuma shi ne ziyararsa ta farko da ya yi zuwa kasashen duniya tun bayan hawansa karagar mulki a karshen watan Yuli.