Pezeshkian: Dole ne Amurka ta tabbatar da cewa da gaske take yi a game da tattaunawa

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin wata ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa da manyan kungiyoyi a kasar, inda ya tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen harkokin mulki, da manufofin harkokin waje, da kalubalen tattalin arziki da zamantakewar kasar.

Da yake magana game da kalubalen gudanar da harkokin mulki, shugaban na Iran ya bayyana cewa, ba za a iya cimma gyara halayen kungiyoyi da bangarorin gwamnati ta hanyar canza daidaikun mutane ba, sai dai hakan yana bukatar “sauyi na dabi’un hukumomi na dogon lokaci,” yana mai jaddada cewa, “sauyi na hakika yana daukar shekaru goma.

Dangane da batutuwan da suka shafi zamantakewa, Pezeshkian ya jaddada cewa ba za a iya magance rikice-rikice ta hanyar ba da umarni kadai ba, yana mai bayanin cewa gwamnati na da shirye-shirye don magance matsalolin da suka hada da karancin makarantu, tsadar rayuwa, rashin aikin yi, da rashin daidaiton tattalin arziki, amma “bai takaitu ga samar da shirye-shirye kawai ba.

Dangane da manufofin ketare kuwa, ya yi nuni da cewa, Iran ta tattauna da dukkan shugabannin kasashen yankin a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Sallah, inda ya jaddada cewa, dangantakar da ke tsakaninta da kasashen da ke makwabtaka da ita ta inganta idan aka kwatanta da baya.

Amma ya kara da cewa, “Tattaunawa da Amurka wani lamari ne na daban,” yana mai bayanin cewa, “Lokacin da Washington ta matsa mana lamba kuma ta ci gaba da barazanarta, ta yaya za mu yi shawarwari da ita?”

Shugaban na Iran ya yi nuni da cewa, matsayin kasarsa na lumana kan amfani da makamashin nukiliya, ba wai kawai maganganun siyasa ba ne, a’a, a maimakon haka a kan wata fatawa ta addini da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fitar ne, wadda ta haramta amfani da makamashin nukiliya ta hanyoyi da ba na ayyukan farar hula ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments