Isra’ila Ta Kara Tsananta Hare-Hare A Kan Gaza

Sojojin HKI sun kara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Falasdinawa a Gaza, a dai-dai lokacinda ake kiranta zuwa tsagaita wuta a gazar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar kare fararen hula ta falasdinawa a Gaza, tana fadar haka a safiyar yau Talata. Ta kuma kara da cewa, Ta kuma […]
Trump Yayi Barazanar Karawa China Kashi 50% Na Kudaden Fito

Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi barazanar karwa kasar China kasha 50% na kudaden fiton da zata karba daga kayakin kasar China da zasu shiga kasar, idan har bata janye maida martanin da tayi na kasha 34% dai dai karin kudin fito da Amurka ta kara mat aba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran […]
Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Dangane Da Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran […]
Yan Sanda A Saudiya Sun Tsare Wata Bafalasdinya Saboda Bayyana Tutar Kasarta A Kan Jakarta A Masallacin Ka’aba

Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin […]
Gwamnatin Kasar Aljeriya Ta Dakatar Da Zirga-Zirgan Jiragen Saman Kasar Zuwa Kasar Mali

Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar. Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi. Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe […]
Pezeshkian: Dole ne Amurka ta tabbatar da cewa da gaske take yi a game da tattaunawa

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin […]
Gaza: Isra’ila ta kashe Dan jarida bayan kona shi da ransa

A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi […]
Saudiyya ta bayar da wa’adin ficewar dukkanin masu aikin Umrah daga kasar

Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin […]
Najeriya: An gudanar da zanga-zangar adawa da wasu shirye-shiryen gwamnati

An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta. […]
Iran da Amurka zasu fara tattaunawa ranar Asabar a Oman

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar […]
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Aljeriya da kasashen kawancen Sahel

A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo […]
Faransa, Masar da Jordan sun bukaci tsagaita wuta a Gaza

Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin. Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a […]
An sake zanga-zangar kin jinin gwamnatin Netanyahu a Tel-Aviv

A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar […]
Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa

Jamhuriyar Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa, yayin da Faransanci ya zama harshen aiki mai sauki, don haka, Faransanci ba yaren hukuma ne ba. Matakin dai ya dogara ne da shawarwarin da babban taron kasar ya gabatart a watan Fabrairu, wanda kuma shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya amince da shi a […]