Sojojin kasar Pakistan sun bada labarin kakkabo jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daganesa wato Drones wadanda suka fito daga kasar Afghanistan kuma ta lalatasu.
Jaridar Arab News ta nakalto majiyar kasar Pakisatan na fadar haka a yau Laraba, kuma ta kara da cewa, wannan ya nuna cewa gwamnatin kasar Afghanistan tana goyon bayan yan tawayen kasar wadanda suke aiwatar da ayyukan ta’addanci a yankin sitan Baluchistan na kudu masu arewacin kasar.
Kafin haka majiyar sojojin kasar Pakistan ta bada labarin aiwatar da hare hare cikin kasar Afghanistan, a matsayin maida martani kan wasu hare haren wanda wata kungiyar mai suna Jama’atul Ahrar wani bangare na Taliban Pakistan ta dauki alhakin kaiwa kan birnin Karachi na bakin ruwa.
Islamabad tace sojoji 29 ne suka rasa rayukansu, kuma ta fadawa wani jami’in diblomasiyyar Afganistan kan cewa afghanawa suna daga cikin wadansa suka kai hare haren na Karachi. Gwamnatin Afghanistan ta musanta labarin.