OIC Ta Yi Maraba Da Shirin Gwamnatocin Larabawa Na Sake Gina Zirin Gaza

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, Hussein Ibrahim Taha, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga shirin Larabawa na sake gina zirin Gaza.

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, Hussein Ibrahim Taha, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga shirin Larabawa na sake gina zirin Gaza.

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta gudanar da wani zama na musamman na majalisar ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar, taron da ya gudana a birnin Jeddah na kasar Saudiyya a wannan  Juma’a, inda suka tattauna halin da ake ciki dangane da ayyukan wuce gonad a iri na Isra’ila a Falastinu.

A cikin jawabinsa, Sakatare-Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin sake gina zirin Gaza, wanda taron kolin kasashen Larabawa ya amince da shi, tare da jaddada hakkin al’ummar Palasdinu na ci gaba da zama a cikin kasarsu.

Baya ga haka kuma ya yi gargadi dangane da hadarin da ke tattare da matakan da Isra’ila take shirin dauka na korar Falastinawa daga yankunansu a Gaza, da kuma mamaye wasu yankuna a gabar yammacin kogin Jordan, yana mai cewa kungiyar OIC ba za ta taba  amincewa da hakan ba.

Babban magatakardar na kungiyar OIC ya jaddada cewa, ba za a iya raba ko kuma maye gurbin hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu wato (UNRWA) da kuma muhimmiyar rawar da take takawa wajen yi wa miliyoyin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa hidima ba, yayin da ya jaddada bukatar a rubanya tallafin siyasa da kudade ga wannan hukumar.

Babban magatakardar ya yi kira da a kara kaimi wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da janyewar sojojin mamaya gaba daya daga Gaza, da kuma isar da kayayyakin jin kai ga al’ummar yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments