Oficin Jakadan Iran A MDD Ya Ce Babu Wani Sako Da Ya Karba Daga Shugaban Kasar Amurka

Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal

Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi Khaminae wasika, inda a ciki yake kiransa zuwa tattaunawa da Amurkan a kan shirin makamashin Nukliyar kasar Iran.

Har’ila yau shugaban ya bayyana haka wa tashar talabijin ta Fox news. Iran dai ba ta son tattaunawa kai tsaye da Amurka saboda rashin gaskiya a cikin al-amuransu. Musamman shi Donal Trump, sabo da shine ya fidda kasarsa daga yarjeniyar JCPOA tun farko sannan ya dage sai ta sake tattauna da Iran sabowayar yarjeniya.

Kafin haka dai jagoran ya bayyana cewa, tattaunawa da Amurka a dai dai lokacinda take takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki, ba zai yu ba, saboda daukan kaskanci ne wanda bai dace da JMI.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya jaddada goyon bayansa ga ra’ayin Jagoran dangane da tattaunawar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments