Nuril Maliki: Ba Zan Janye Daga Takarar Zama Fira Ministan Iraki Ba

A wata hira da ya yi da  kamfanin dillancin labarun Faransa, a yau Litinin Nurul Maliki na Iraki  ya ce, ba zai janye daga tsayawa

A wata hira da ya yi da  kamfanin dillancin labarun Faransa, a yau Litinin Nurul Maliki na Iraki  ya ce, ba zai janye daga tsayawa takarar zama fira ministan kasar ba.

Haka nan kuma Nuril Maliki ya fadi cewa; Suna bai wa Amurka tabbacin cewa, za a kwance damarar makaman duk wata kungiya, ya zaman jami’an tsaro ne kadai ke rike da su.

Akan alakar kasar Iraki da Iran kuwa, Nurul Maliki ya ce, alakar kasashen biyu dai an gina ta ne akan maslaha.

Nurul Maliki wanda kawance ‘jam’iyyun siyasa na shi’a ya tsayar da shi a matsayin dan takararsu na zama Fira minista, ya fuskanci suka daga kasar Amurka wacce shugabanta Donald Trump ya bayyana cewa; za su dakatar da taimakon da suke bai wa Irakin idan har aka zabe shi.

Donald Trump ya rubuta a shafinsa na “Social Trust” cewa: Idan Maliki ya zama Fira ministan Iraki, to Amurkan za ta dakatar da taimakon kudaden da take bai wa kasar.

Kudaden Iraki da take sayar da man fetur a kasuwannin duniya suna shiga cikin Baitul-malin Amurka ne kai tsaye gabanin su isa ga babban Bankin kasar ta Iraki, lamarin da ya sa Amurka take da girma tasiri ta fuskar tattalin arzikin Iraki.

Da yake mayar da martani akan jita-jitar dake cewa, ya jami’iyyarsa ta ” Daulatul-Qanun” ta janye shi, a matsayin dan takara, ya kore hakan. Wasu kafafen watsa labarun na kasar Iraki sun kore wata jita-jitar da ake watsawa dakecewa, Shugaban Tayyarul-Hikima” Sayyid Ammar Hakim ya kafa wani kawance na jam’iyyu hudu domin janya sunan Nurul Maliki a matsayin dan takarar Fira Minista.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted