Nukiliya : Iran ta kirayi mai kula da harkokin Ostiriya da ke birnin Tehran kan wasu kalamai na tsokana

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi babbar mai kula da harkokin kasar Ostiriya da ke birnin Tehran domin nuna rashin amincewa da zarge-zargen data

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi babbar mai kula da harkokin kasar Ostiriya da ke birnin Tehran domin nuna rashin amincewa da zarge-zargen data danganta da na ‘’tsokana” da hukumar leken asirin cikin gidan kasar ta Turai ta yi dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Shugaban ofishin sashen yammacin Turai na ma’aikatar harkokin wajen Iran Alireza Molaqadimi ya gayyaci Michaela Pacher a ranar Juma’a, inda ya nuna bacin ran kasar iran game da zarge-zargen.

A cikin rahotonta na shekara-shekara kan barazanar da duniya ke fuskanta, hukumar leken asiri ta kasar Ostiriya (DSN) ta yi ikirari a ranar Litinin cewa Iran na ci gaba da aiwatar da shirin kera makaman nukiliya tare da fadada karfinta na makamai masu linzami.

M. Molaqadimi ya yi watsi da wannan zargi mara tushe, yana mai jaddada cewa ya sabawa rahotanni da dama da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta fitar.

Ya ce shirin nukiliyar kasar Iran ya yi daidai da alkawurran da kasar ta doka karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta NPT, ya kuma yi kira ga gwamnatin Ostiriya da ta yi bayani a hukumance kan wannan batu.

Tun da farko dama a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya yi watsi da rahoton da ya ce na “karya ne kuma marar tushe” da hukumar leken asirin ta Austria ta fitar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments