Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu

Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da

Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Abuja.

Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa da muhimmanci tsakanin bangarorin biyu.

A  yayin taron, wakilan bangarorin biyusun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a duniya, musamman yaƙi da ta’addanci, da kuma inganta hulɗar siyasa da tattalin arziki.

Ministocin biyu sun jaddada aniyarsu ta yin aiki tare wajen samar da bayanai na sirri kan barazanar ta’addanci a duniya, musamman kan hanyoyin samar da kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin ta’addanci.

Najeriya na daga cikin kasashe masu alaka mai karfi tsakaninsu da Isra’ila, musamman a bangarorin da suka shafi batutuwan tsaro da kuma noma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted