Mutane Kimani Dozen Guda Sun Mutu A Tashin Bom A Pakistan

Tashin bom wanda ake zaton yan ta’adda suka sanya a cikin wata Motota a kusa da ofishin yansanda a garin Koha na lardin Khybar Pakhtunkhuwa

Tashin bom wanda ake zaton yan ta’adda suka sanya a cikin wata Motota a kusa da ofishin yansanda a garin Koha na lardin Khybar Pakhtunkhuwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masallata da yansanda 15 da kuma raunata wasu kimani 50.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dan rahotunta a yankin yana cewa an kashe yan ta’adda 10 a musayar wuta bayan hare hare sannan sojojin Pakistan 6 suka rasa rayukansu.

Labarin ya ce bondin ya tashi ne a dai dai lokacinda ake sallar jumma’a a cikin wani masallaci kusa da inda ofishin yansanda a garin yake.

A dai dai lokacinda ake gudanar da bincike don sanin wadanda suka kai hare haren, sojojin kasar sun bayyana cewa ana zaton wata kungiyar yan ta’adda wacce ake kira Tahrir Taliban –Pakistan (TTP) suka kai hare hare. Gwamnatin kasar Pakistan tana kirinsu fitinannu khawarijawa’.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted