Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Rage farashin Man Fetur

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaba kasa a zabe mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rage

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaba kasa a zabe mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rage farashin man fetur saboda yan Najeriya su numfasa.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto tsohon mataimakin shugaban kasar yana fadar haka a yau a Abuja babban birnin kasar, a lokacinda yake jawabi kan tsadar manfetur wanda ya takurawa yan kasar tun lokacinsa Tinubu yah au kan kujerar shugabancin kasar a shekara ta 2023 har zuwa yau.

Atiku ya kara da cewa, a shirye yake ya gabatarwa shugaban wasu shawarorin dangane da yanda zai sawwakawa yan kasar wahalan da suke ciki. Ya yarda gwamnatin Tinubu ta ya alfakhari da shawarar idan ta yi aiki.

Ya kumakara da cewa, miliyoyin yan Najeriya kama daga kungiyar Kodago, dillalan manfetur, da wasu da dama sun yi magana kan halin da mutanen kasar suke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted