Mutanen Yemen Sun Fito Kan Tituna Don Goyon Bayan Sojoji

Mutanen Yemen a duk jihohin kasar sun fito gangamin goyon bayan sojojin kasar wadanda suka sami nasarori masu yawa, a kan sojojin hayar saudia da

Mutanen Yemen a duk jihohin kasar sun fito gangamin goyon bayan sojojin kasar wadanda suka sami nasarori masu yawa, a kan sojojin hayar saudia da Hadaddiyar daular Larabawa wadanda suke rike da wani bangare kasar tun shekara ta 2015. Haka ma sun kai hare hare da makamai daban daban a cikin kasar ta saudia inda suka lalata kayakin kamfanin Aramco na man fetur na kasar. Har’ila yau sojojin kasar sun hana jiragen ruwan daukar man fetur na kasar saudiya amfani da mashigar ruwa ta babul Mandam mai matukar muhimmanci ko kuma amfani da tekun Red Sea, sai idan ta daukewa kasar takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata.

Saudia da kawayenta sun shiga yaki da kungiyar Ansarullah tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu rabu hadi Mansur kan kujerar shugabancin kasar, amma sun kasa yin haka har suka tsagaita wuta a shekara ta 2022, amma kuma saudia ta ci gaba da dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har na kusan shekaru 12.

A halin yanzu Mutanen Yemen suna son saudia ya kawo karshen takunkuman  tattalin arzikin da ta dorawa kasar na tsawon kimanin shekaru 12.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted