Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Nujaba na kasar Iraki ya ce bin hanyar diblomasiyya da kasar Saudi aba zai yu ba, sai an yi amfani da karfi.
Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Sheikh Akram Al-Kaabi yana fadar haka haka ya kuma kara da cewa, bisa irin abinda aka jarraba da kasar Saudia, ba’a fahintar juna da ita ta hanyar diblomasiyya,. Sai an nuna mata karfi. Ya kuma zargi kasar Saudia da hannu dumu dumu a duk ayyukan ta’addancin da aka aikata a kasar Iraki tun bayan mamayar da Amurka da yiwa kasar a shekara 2003.
Ya ce kasar Saudia ce ta ke bada kudade da makamai gay an ta’adda masu kafirta musulmi wadanda suka yi ta tada boma bomai a cikin kasar Iraki a shekarun da suka gabata, kuma sun ci gaba da yiwa mutanen kasar Iraki makirce –makirce masu yawa. Saudia tana da hannu a zubar da jinin dubban daruruwan Irakawa, wadanda basu san hawa ko sauka ba.
Yace amfani da karki kan kasar Saudia ne kawai zai iya zama fansa kan mahuntan kasar Saudia saboda jinin mutanen kasar Iraki da ta zubar, musamman dakarun Hashdu Shaabi wadanda suka kawo karshen ikon kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta ta kafa a Iraki.