Shekaru 28 Da Sahadar Jami’an Diblomasiyyar Iran A Afganistan

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sha alwashin nema da kuma gano wadanda suka kashe jami’an diblomasiyyar kasar guda 8 da kuma wani dan jarida

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sha alwashin nema da kuma gano wadanda suka kashe jami’an diblomasiyyar kasar guda 8 da kuma wani dan jarida a karamin ofishin jakadancin kasar da ke Mazar Asharif na kasar Afganistan.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran, ya nakalto ma’aikatar tana fadar haka a dai dai lokacinda take juyayin tunawa da shahadar wadan nan jami’an diblomasiyya na kasar wadanda yan ta’adda dauke da makamai suka kashe a karamin ofishin jakadancin kasar dake mazar Ashasharif a ranar 8 ga watan Augustan shekara 1998.

Bayanin ya kara da cewa yau shekaru 28 kenan da kashe wadan nan jami’an diblomasiyyar kasar da kuma dan Jirada na kamfanin dillancin labaran IRNa na gwamnatin kasar.

Kuma sun hada da Heidar-Ali Bagheri, Mohammad-Ali Qiyasi, Majid Nouri Niaraki, Nasser Rigi, Noorollah Norouzi, Karim Heydarian, Rashid Pariyav Fallah, da kuma  Mohammad-Nasser Naseri, sai kuma dan jirida guda mai suna Mahmoud Saremi, na kamfanin dillancin labaran IRNA.

An sanya ranar yan jaridu ta kasa ta zama ranar shahadar dan Jiridar ta IRNa ne, wanda kashe shi da jami’an diblomasiyyar kasar ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted