Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasarsa zata ci gaba a kan tafarkinta na jajircewa don kare hakkin mutanen kasar duk tare da matsin lamba daga kasashen duniya da dama.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau Lahadi. A wani jawabinda da ya gabatar a makarantar koyin aikin siyasa da al-amuran kasa da kasa na ma’aikatar harkokin waje da ke nan birnin Tehran. Inda ya gabatar da jawabi mai suna muharram da Ashura a mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran.
Aragchi ya kara da cewa, Ashura a ayyukan diblomzasiyya ya zama babbar misali ga ma’aikatan diblomzasiyya a ma’aikatarsa, saboda da shi ne suke jajircewa kan gaskiyan da suka amince da ita kuma suke kanta.
Saboda Ashura ce jami’an diblomasiyyar kasar suka zama abin buga misala wajen dagewa kan neman hakkin mutanennsu wadanda suke wakilta a ko ina suka je a duniya.