Iran Ta Bayyana Sharuddan Sake Bude Hurmuz

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya sake nanata sharuddan majalisar na sake bude mashigar ruwa ta Hurmuz . Kamfanin dillancin labaran IP na

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya sake nanata sharuddan majalisar na sake bude mashigar ruwa ta Hurmuz .

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Baqer Zolqdr yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa Iran ba zata sake bude mashigar ruwa ta Hurmuz ba sai Amurka ta canza halayenta dangane da kasar.

Zolqadr ya kara da cewa JMI ba zata sake amincewa a yi amfani da mashigar ruwa ta Hurmuz ko wata hanya don barazana ga tsaron kasar ko cin mutuncin addininta. Ya kuma kara da cewa dole ne a kawo karshen ayyukan ta’addancin da ke faruwa a kasashen Yemen Iraki da kuma Lebanon.

A wani bangare na bayanin Zolqadr ya ce dole ne a kawo karshen killace ruwayen kasar Iran daga kudancin kasar ta ruwa da kuma kasa.

Daga cikin abubuwan da ya ambata na sharuddan bude mashigar har da biyyan diyya kan barnan da aka yiwa kasar Iran a yake yake guda biyun da aka dora mata, da sake kudaden kasar da aka rike su a bankunan kasashen waje. Da kuma dauke dukkan takunkuman da aka dorawa JMI.

Daga karshe yace wannan shi ne bukatun mutanen kasar Iran kuma saboda su ne suke fitowa kan tituna tun farkon yakin ya zuwa yanzu.

Zolkadar ya bayyana cewa Iran ba zata jada baya a kan wadannan bukatu ba, ko a fagen fama ko kuma a teburin tattaunawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted