Hukumomin Namibiya sun hana wani jirgin ruwa da ke jigilar kaya zuwa “Isra’ila” shiga cikin yankin kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da yin kisan kare dangi a Gaza, wanda yanzu ya rage ‘yan makonni ya cika shekara guda.
Ministar shari’a a Namibia Yvonne Dausab ta tabbatarwa kafar yada labaran kasar ta New Era cewa, jirgin mai suna MV Kathrin, an dakatar da shi ne saboda dakon kaya da yake yi da suka hada da bama-bamai da nufin kai su Isra’ila.
Dausab ta kara da cewa, an dakatar da jirgin ne bisa goyon bayan Namibiya ga al’ummar Palasdinu da kuma kiran da kasar ta yi na ganin an kawo karshen yakin Gaza.
Da take ambaton binciken da ‘yan sanda suka gudanar, ta ce jirgin MV Kathrin “hakika yana dauke da ababe masu fashewa da ake nufin isa da su zuwa Isra’ila, don haka an hana shi shiga ruwan Namibiya”.
“Namibiya ta zabi daukar matsaya ta kin goyon bayan ko shiga cikin laifukan yaki na Isra’ila, da laifukan cin zarafin bil’adama, da kisan kiyashi, da kuma mamayar da ta yi wa Falasdinu ba bisa ka’ida ba.”
Jirgin, wanda ya tashi daga Vietnam, ya nemi izinin shiga tashar jiragen ruwa ta Walvis Bay kafin ya ci gaba da tafiya arewa mai yiwuwa zuwa Bahar Rum ta mashigar Gibraltar.