Najeriya: Hukumar Zabe Ta Fara Rijistan Masu Zabe Karo Na Biyu

Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta fara rijistar masu zabe wanda ake ira CVR a karo na biyu bayan da ta kammala

Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta fara rijistar masu zabe wanda ake ira CVR a karo na biyu bayan da ta kammala aikin a karo na farko a cikin ranar 10 ga watan Decemban da ta ya gabata.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa hukumar ta INEC ta fara rijistan farko a kan internet a ranar 18 ga watan Augustan shekara ta 2025 sannan ta fara nag aba da gaba a ranar 25 ga watan a duk fadin kasar, sannan ta kammala zagaye na farko a cikin watan Decemba.

Kwamishina mai kula rijistan ya bayyana cewa a shafukan Internet mutane 9,891,801 ne suka cikita sunayensu don rijista na karshe. Daga cikin su, zuwa watan Decemba mutane miliyon 2,572,054 sun kammala rijistansu. Daga cikinsu miliyon 1,503,832 sun kammala rijista a shafukan internet sannan wasu miliyon 1,068,222 kuma sun kammala rijista na gaba da gaba.

Daga karshe kwamishinan ya bayyana cewa an dakatar da aikin rijistar samun katin zabe a Abuja da kuma jinar Amambra saboda zabubbukan da aka gudanar a yankunan, sannan nan gaba za’a bada sabon lokaci na yin rijista a jihar da kuma Abuja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted