Hukumar zaben kasar ta kasar Guinea-Bissau ta sanar a jiya Talata cewa sabon tsarin mulkin da al’ummar kasar sun amincea da sabon tsaron mulkin da su ka kada kuri’a akansa.
Amincewa da sabon kundin tsarin mulkin dai yana a matsayin share fage ne na manyan zabukan da za a yi a kasar a wannan shekarar, wanda kuma zai bai wa shugaban da za a zaba Karin iko fiye da baya.
Kada kuri’ar da al’ummar kasar su ka yi a ranar Lahadin da ta gabata an yi ne bayan kasa da watanni 10 daga juyin mulkin soja. Za kuwa a yi manyan zabukan kasar ne a ranar 6 ga watan Disamba na wannan shekarar.
A karkashin sauyin da aka yi wa tsarin mulkin kasar ta Guinea-Bissau, an cire yawan shekaru shugaban kasa,ko kuma tsawon wa’adin da mai mulkin za iyi.
Wasu kasashen nahiyar Afirka da aka yi irin wadannan sauye-sauyen na cire tsawon lokacin Mulki sun hada Zimbabwe,Guinea, Togo, Uganda da kuma Chadi.
Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar a jiya Talata ya kunshi cewa, kaso 70% na wadanda su ka kada kuri’ar raba gardamar, sun amince da sauye-sauyen da aka yi.
A nan gaba kadan ne ake sa ran cewa za a fitar da sakamakon karshe da kuri’ar raba gardamar a gaban kotun kolin kasar.
Ya zuwa yanzu dai babu wani koke da kotuna su ka karba akan zaben raba gardamar da aka yi.
Tun da wannan kasa ta sami ‘yanci a 1974, an yi juyin mulki har sau biyar da na karshensa shi ne na watannin bayan nan.