Kamfanin kasar Rasha na Nukiliya ya bayyana cewa a halin yanzu suna tattaunawa da Iran domin gina wasu sabbin kananan cibiyoyin Nukiliya.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto shugaban zartarwa na kamfanin “RusAtom Alexey Likhachev yana cewa: Rasha ta gabatarwa da Iran tsarin aikin gina kananan cibiyoyin na Nukiliya.
Haka nan kuma Alexey Likhachev ya ce; Idan zaman lafiya ya dawo Iran za ta ci gaba da bunkasa cibiyoyinta na Nukiliya domin amfani da su wajen samar da wutar lantarki.