Farashin Makamashi Ya Shafi Amurkawa Masu Biyan Haraji

Bayan fara yaki a kan kasar Iran watanni 6 da suka gabata, a halin yanzu yakin ya shiga wata na 7 kuma babu alamun karewarsa

Bayan fara yaki a kan kasar Iran watanni 6 da suka gabata, a halin yanzu yakin ya shiga wata na 7 kuma babu alamun karewarsa nan kusa.

Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta bayyana cewa shugaban Trump yayiwa Amurkawa alkawalin ba zai shiga yake yake a duniya ba, kuma yaki a kan kasar Iran ba zai wuce kwanaki mo makonni ba Iran zata mika kai. Amma gashi an shiga wata na 7 da fara yakin Shugaban bai san hanyar kawo karshensa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, banda kasancewar wannan yakin shi ne yaki wanda Amurka suka fi kyamarsa ya zuwa yanzu sun kashe $800 kare a daga aljihunsu kan makamashi kadai. Kuma ba’a san karshensa ba.

A ranar 28 ga watan Fabrairu na wannan shekarar ne Sojojin Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki a inda suka fara kashe Jagoran Juyin juya halin musulunci a kasar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei (q) da iyalan gidansa a cikin gidansa. Sannan suka kashe manya-manyan Jami’an gwamnatin kasar da sauran mutane.

Wannan tare da kawo karshen gwamnatin kasar a cikin yan kwanaki ko makonni idan sun yi yawa. Amma hakan ya gagara kuma babu alamun zata iya yin haka nan kusa ko nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted