IRGC Sun Cilla Makamai Kan Gidajen Kwamandojin Amurka

Dakarun IRGC a nan Iran sun cilla makaman Drones da kuma masu linzami kan sansanin sojojin Amurka mai suna Al- Al-Salem a kasar Kuwait inda

Dakarun IRGC a nan Iran sun cilla makaman Drones da kuma masu linzami kan sansanin sojojin Amurka mai suna Al- Al-Salem a kasar Kuwait inda suka fada kan gidajen gwamnadojin sojojin Amurka a sansanin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar IRGC na cewa sojojinsu na kasa sun cilla makamai masu linzami da kuma Drones kan gidajen kwamandojojin sojojin sami na Amurka na Ali Al- Alsalen a kasar Kuwait  a safiyar yau Laraba.

Majiyar ta nakalto jami’in watsa labarai na rundunar yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hare hare maida martani ne ga wanda sojojin Amurkan suka kai tsibirin Sirik wanda yayi sanadiyyar shahadar mutane 4, daya daga cikinsu yaro  ne. Sannan wasu 70 kuma sukaji rauni. Wannan ma ya shiga cikin ayyukan ta’addanci da kashe fararin hula wanda gwamnatin Trump ta aikata a wannan yakin wanda ya kai watanni 6 ahalin yanzu.

Labarin ya kara da cewa makaman Amurka a wannan karon sun fada a kan bikin aure ne da ake gudanarwa yankin. Ta kuma kara da cewa da wannan dalilin ne dakarun na IRGC suka maida martani a sansanin Ali Al-Salim na Kuwait.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted