IRGC:  Amurkawa ‘Yan Ta’adda Su Kwana Da Sanin Cewa Al’ummar Iran Ba Ta Tsoron Wasan Wuta

Ya ku al'ummar musulmin Iran, tsayin Dakar da kuke yi a cikin wuraren taruka wani lamari ne da ya karfafa zukatan al'ummu,kuma duniya tana ganin
Mashigar Hurmuz

A wata sanarwa mai lamba ta 8 da Irgc su ka fitar, ta kunshi bayani ga al’ummar Iran dake cewa:

” Da Sunan Allah Mai Karya Kashin Bayan Masu Girman Kai

Ku yake su,har sai fitina ta kare, ya zamana dukkanin addini na Allah ne.”

Ya ku al’ummar musulmin Iran, tsayin Dakar da kuke yi a cikin wuraren taruka wani lamari ne da ya karfafa zukatan al’ummu,kuma duniya tana ganin yadda ku ka kasance a farko da yadda kuke makure masu girman kai, manyan masu aikata laifi.

A daren jiya, sojojin ta’addanci na Amurka sun sake aikata da aiwatar da laifukan ta’addanci akan bikin aure domin sake nuna halayyar keta da mugunta da dabbanci da kuma firgita mutane. Sai dai kuma sun mance cewa al’ummar Iran ba ta tsoron wasan wuta, kuma su san cewa wannan zamani ba irin na baya ne da ake kaskantar da al’ummu ba a sa su mika wuya.”

Sanarwar ta dakarun kare juyin musulunci ta ci gaba da  fadawa Amurkawa cewa, Duniya ta farka daga bacci, kuma wannan karni ne da al’ummun duniya za su yi galaba.

Har ila yau dakarun IRGC sun ce, komai tsananin halayyar dabbancin da Amurka za ta nuna, ba zai raunana kulle mashigar Ruwan Hurmuz da Iran ta yi ba.

Haka nan kuma sanarwar dakarun na IRGC sun fada wa al’ummar Iran cewa; Muna sanar da ku cewa, sa’o’i kadan da su ka gabata, wasu jiragen Ruwa biyu na dakon man fetur sun fashe,bayan da Amurka su ka yi musu busa a kunne cewa su ratsa ta wata hanyar da ta sabawa doka, ta ci karo da nakiyar ruwa, a halin yanzu kuwa suna ci da wuta.

Tun da fari dakarun IRGC sun yi gargadin cewa da akwai nakiyar ruwa akan hanyoyin da da su ka sabawa doka, sannan kuma an hana duk wani jirgin ruwa da Amurka take yaudara wucewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted