Akalla mutane 12 suka yi shahada a hare haren makaman Amurka a wurare daban daban a kudancin kasar a daren Talata. A Sirik da kuma Hurmuzghan. Banda haka wasu mutane 7 sun yi shahada sannan wasu sun ji rauni a wasu hare haren na Amurka a garin Ahwaz da kuma Aghajari na Lardin Khuzistan a kudancin kasar Iran.
Hukumar CENTCOM na Amurka ta bada sanarwan cewa ta kai hare haren ne kan sansanin sojojin IRGC.
Kakakin dakarun Khatamul Ambiya Ibrahim Zulfikar ya ce sanarwan da CENTCOM ta bayar na cewa kafin haka IRGC sun hana wani jirgin ruwan farar hula wucewa ta mashigar ruwa ta Hurmuz. Sannan sun kai hare hare kan sojojin Amurka a yankin.
Ya kuma kara da cewa dakarun Khatamul Anbiya sun maida martani kan sansanonin sojojin Amurka a yankin yammacin Asia wadanda suka hada da sansanin Ali Alsalem a kasar Kuwai da kuma wasu sansanonin a kudancin kasar Jordan.