Shugaban cibiyar sararin samaniya ta Iran ya bayyana cewa; Sun shirya tsaf domin harba sabbin taurarin dan’adam kirar Iran mai suna “Pars 2”.
Kamfanin dillancin labarum “Mehr” ya nakalto Hussain Salariyah yana cewa; Hotunan tauraron dan’adam na “Khayyam” da yake aikowa daga sararin samaniya ana amfani da su, wajen sabunta taswira, kuma an bai wa kamfanin gidan waya na kasa kaso 25% na jumillar hotunan domin amfani da su.
A halin da ake ciki Iran tana ci gaba da bunkasa wasu taurarin dan’adam din domin harba su sararin samaniya daga cikinsu da kawai “Paris 2” da kuma wasu 24 a karkashin rukunin taurarin dan’adam masu sunan “Shahid Sulaimani.”.