Sojojin kasar Iran sun kakkabo jirgin yaki samfurin MQ 9 na kasar Amurka a kan garin Khomain a cikin lardin Markazi na kasar a jiya Talata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin sun kakkaboshi da sabbin makaman kare sararin samaniyar da suke da su, ba tare da wani karin bayani ba.
Wannan yana zuwa ne bayan hare haren da sojojin Amurka suka kai baya bayan nan a wasu wurare a gaban tekun farisa, a daren talata.
Har’ila yau kafin haka rundunar CENTCOMD ta Amurka a yankin Asia ta bayyana cewa ta fara kaiwa kasar Iran hare hare.
Tun lokacin fara yakin a karshen watan Fabrayru na wannan shekarar, wannan shi ne karo na uku da suke komawa yaki. Bayan da Amurka ta yi watsi da yarjeniyar fahintar juna da ta Islamabad.